NDLEA ta yi nasarar cafke dillalan miyagun ƙwayoyi 231 a jihar Oyo

NDLEA ta yi nasarar cafke dillalan miyagun ƙwayoyi 231 a jihar Oyo

  • Hukumar NDLEA ta ce ta mutane kama mutane 231 da ake zargin masu safarar miyagun kwayoyi a jihar Oyo
  • Kwamandan NDLEA na jihar ta ce 215 cikin wadanda ake zargin maza ne yayin da 16 kuma mata ne
  • Hukumar ta NDLEA ta yi holen wanda ake zargin ne gabanin ranar yaki da miyagun kwayoyi na duniya na bana a ranar 26 ga watan Yuni

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, reshen jihar Oyo, ta ce ta kama mutane 231 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi daga watan Yunin 2020 zuwa Yunin 2021, Pulse NG ta ruwaito.

Da ya ke yi wa yan jarida jawabin, a ranar Alhamis game da ayyukan da hukumar ta yi cikin lokacin da ake nazari, Josephin Obi, kwamandan jihar ya ce mutum 215 cikin wadanda ake zargin maza ne yayin da 16 kuma mata.

Jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA.
Jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA. Hoto: The Punch

DUBA WANNAN: Dakatar da Twitter ya hana wa gwamnonin PDP kafar yaɗa labaran ƙarya, Fadar Shugaban ƙasa

Mrs Obi, wacce ta samu wakilcin mataimakin kwamanda Anthony Gotar ta kuma ce rundunar ta yi nasarar kwace ganyen wiwi mai nauyin 6,355.74 da wasu kayan maye a cikin watanni shida.

Ranar yaki da miyagun kwayoyi na duniya

Kamfanin dillanin labarai na kasa, NAN, ya ruwaito cewa taron manema labaran na cikin abubuwan da aka yi ne domin ranar Yaki da Safarar Miyagun kwayoyi da shansu na 2021 da za a yi a ranar 26 ga watan Yuni.

Taken bikin ranar na wannan shekarar shine : 'Yada gaskiya game da kwayoyi, Ceto rayyuka.'

Obi ta ce ta'amulli da miyagun kwayoyi babban barazana ce ga matasa duba da cewa masu aikata laifukan suna kara bullowa da sabbin dabaru.

"Yana da muhimmanci a yadda wannan gaskiyar musamman duba da yadda abubuwan da ba a saba gani ba ke bullowa.
"Babban kallubalen yanzu shine ana saka muggan kwayoyi cikin abubuwa kamar biskit ana siyarwa a gari.
"Ku rika lura da abin da kuke ci a wurin biki, musamman matasa," a cewar kwamandan na NDLEA.

A wani labarin daban, Hukumar Yaki Da Hana Safarar Miyagun Kwayoyi na Kasa, NDLEA, ta ce ta kama wasu mutane da ake zargi da safararmiyagun kwayoyi a birnin tarayya Abuja, The Cable ta ruwaito.

Femi Babafemi, kakakin NDLEA, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi ya ce an kama su ne sakamakon samamen da hukumar ta yi cikin wannan makon.

Cikin wanda aka kama akwai wata Ese Patrick da ake zargi na siyar da miyagun kwayoyi a dandalin Instagram.

Asali: Legit.ng

Online view pixel