Bayan Mutuwar Kwamishinoni 2, An Fara Addu'o'in Neman Tsari a Jihar Ebonyi

Bayan Mutuwar Kwamishinoni 2, An Fara Addu'o'in Neman Tsari a Jihar Ebonyi

  • Bayan mutuwar wasu kwamishinoni biyu a jihar Ebonyi, an shiga addu'o'in neman kariya
  • Rahotanni a baya sun bayyana cewa, jihar ta i rashin kwamishinoni biyu cikin kankanin lokaci
  • Lamarin ya girgiza gwamnan jihar, wannan yasa ya ba da umarnin fara addu'o'in neman kariya

Rahoto daga jaridar The Nation ya ce, gwamnatin Ebonyi ta fara addu’ar neman kariya na kwanaki uku sakamakon mutuwar kwamishinoni biyu a jihar.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mista Francis Nwaze, mai taimakawa na musamman ga Gwamna David Umahi kan harkokin yada labarai ya fitar a ranar Alhamis.

Addu’ar da aka yiwa lakabi da “Allah ya kare jihar mu da shugabannin mu’’ an shirya ta ne tare da kungiyar kiristocin Najeriya (CAN), reshen jihar ta Ebonyi.

KU KARANTA: Sojoji sun karyata Sheikh Gumi kan cewa jami'ansu na hada baki da 'yan bindiga

Jihar Ebonyi ta yi rashin kwamishinoni biyu a cikin kankanin lokaci, sun fara addu'o'in neman kariya
Gwamnan Jihar Ebonyi, David Umahi | Hoto: legit.ng
Asali: Depositphotos

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa, Nwaze ya ambaci gwamnan yana cewa addu’ar ana yinta ne ga shugabanni a jihar da ma Najeriya baki daya.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Fidelis Nweze, Kwamishinan Bunkasa Ababen More Rayuwa na jihar ya mutu a Asibitin Turkish da ke Abuja a ranar Talata bayan hatsarin mota, jim kadan bayan mutuwar Uche Okah, Kwamishinar Gidaje..

Gwamnan ya bada umarnin a binciki lamarin mutuwar ta Nweze, kamar yadda BBC ta ruwaito a baya.

A jawabinsa, gwamnan ya ce:

“Mun umarci bincike kan mutuwar Nweze. Mun kuma ba da umarnin cewa direbansa da dogarinsa su je ga Kwamishinan ’yan sanda su yi bayani.
“Kwamishinonin biyu ba za a iya maye gurbinsu ba a wurina kuma ina fada da dukkan gaskiya cewa, su masu taimaka min ne ta kaddara; yayin da muke raye, ina fatan mu rayu cikin aminci.''

KU KARANTA: An Kwamushe Wani Sufeton ’Yan Sanda Dake Dillancin Makamai ga ’Yan Bindiga

Hotunan yadda jama'ar Zaria suka yi wa 'yan bindiga sallar Al-Qunuti

A wani labarin, Al'ummar Zaria sun gudanar da Sallar Al-Qunut da addu'oi tsawon mako daya domin neman saukin rikicin 'yan bindiga masu satar mutane da suka addabi yankin.

Dr Shamsuddeen Aliyu mai yasin garkuwan makarantar Zazzau daya daga cikin wadanda suka jagoranci Sallar da addu'oin ya shaida wa BBC cewa an gudanar da sallolin ne a filayen Idi da ke cikin kwaryar Zaria.

Ya ce daruruwan mutane ne suka halarci Sallar da zaman addu'oin domin rokon Allah ya yi maganin 'yan bindiga wadanda ya ce sun yi wa garin Zaria kawanya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.