An Kwamushe Wani Sufeton ’Yan Sanda Dake Dillancin Makamai ga ’Yan Bindiga

An Kwamushe Wani Sufeton ’Yan Sanda Dake Dillancin Makamai ga ’Yan Bindiga

  • Rundunar 'yan sanda a jihar Kuros Riba ta cafke wani jami'inta mai dillancin makamai
  • An kame shi ne tare da wasu mutanen da yake harkallar sayar da bindigogi a yankunan jihar
  • An ce shine jami'in da ke kula da makamai, wannan yasa ya samu damar cin amanar aikinsa

Wani Sufeton ‘yan sanda, Nathaniel Manasseh, ya shiga hannun 'yan sanda a Jihar Kuros Riba bisa zargin dillancin bindigogi da alburusai ga masu aikata laifuka.

An cafke Manasseh a Calabar, babban birnin jihar, kuma aka gabatar da shi a hedikwatar ‘yan sanda ranar Talata tare da sauran wadanda ake zargi da aikata miyagun laifuka, an ce shi babban dillalin bindiga ne kuma ya dade yana wannan harkallar kafin dubunsa ya cika.

Sufeton da ya amsa laifin shi, an ce shi ne ke kula da ma'ajiyar makamai a rundunar 'yan sanda ta jihar kuma an kama shi ne lokacin da ya kasa ba da bahasin wasu kayan aiki ciki har da bindigogin AK-47 guda biyu.

KU KARANTA: Bayan tura Burutai Benin, an tura tsoffin hafsoshin tsaro zuwa wasu kasashe

'Yan sanda sun kame jami'insu dake dillancin makamai ga 'yan bindiga
Jami'in dan sanda a bakin aiki | Hoto: nigeriantribuneng.com
Asali: UGC

Lokacin da aka fara yi masa tambayoyi, ya yi ikirarin cewa an buge shi ne kuma an kwace bindigogin, ciki har da abun hawa, in ji Ripples Nigeria.

Ya bayyana cewa:

“An buge ni kuma an kwace bindigogin. Ba zan iya bayanin zahirin abinda ya faru ba da kuma yadda suka kwace min bindigogin. Ni ba mai harkallar bindiga bane.”

Legit.ng Hausa ta tattaro daga jaridar Nigerian Tribune cewa, kwamishinan 'yan sandan jihar CP Sikiru Akande ya bayyana cewa, Sufeto Manasseh na daga cikin wadanda galibi ke bayar da bindigogin su "haya" ga wasu manyan masu aikata laifuka da kuma 'yan kungiyar asiri.

Akande, yayin da yake gabatar da wadanda ake zargin ya kuma bayyana cewa tun lokacin da sabon kwamandan rundunar yaki da satar mutane da kungiyoyin asiri (AKCTS) ya fara aiki, an kame tarin masu aikata miyagun laifuka.

A cewar CP Akande:

“Kuros Riba tana dawo da martabarta da ta rasa a fannin tsaro kuma a gaskiya, mun kasance jiha mafi zaman lafiya a Najeriya kuma babu abin da zai karya kudurinmu.

KU KARANTA: Matawalle ya gana da Buhari, ya fadi yadda arewa ke farfadowa daga rashin tsaro

Babban Hafsan Sojoji ya kai ziyara Imo, ya ce a ragargaji IPOB ba sassautawa

A wani labarin, Faruk Yahaya, babban hafsan sojojin Najeriya, ya nemi sojojin da aka tura jihar Imo da su rubanya kokarinsu a yaki da haramtacciyar kungiyar IPOB a yankin kudu maso gabas, The Cable ta ruwaito.

Babban hafsan sojojin wanda ya yi kiran yayin da ya ziyarci sojojin ya ce ya zo jihar ne domin a tantance yanayin tsaro yadda yake a jihar.

An kai jerin hare-hare a jihar Imo a makonnin da suka gabata, ciki har da kisan wani jigon jam'iyyar APC, Ahmed Gulak.

Asali: Legit.ng

Online view pixel