Sojoji sun karyata Sheikh Gumi kan cewa jami'ansu na hada baki da 'yan bindiga
- Rundunar sojin Najeriya ta karyata zagin Gumi kan cewa jami'ansu na hada baki da 'yan bindiga
- Malamin ya yi zargin cewa, jami'an tsaro na hada baki da 'yan bindiga wajen aikata laifukansu
- Rundunar soji ta yi kira da Gumi ya zama mai kishin kasa, ya kuma daina watsa zantukan marasa dadi
Rundunar Sojin Najeriya ta karyata zargin Sheikh Ahmad Gumi na cewa jami’anta suna hada baki da ‘yan bindiga wadanda suka kasance masu aikata laifuka daban-daban da cin zarafin da ake yi wa 'yan Najeriya.
Daraktan, Hulda da Jama’a na rundunar, Onyema Nwachukwu, a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, ya mai da martani ga zargin da Gumi ya yi a shirin ARISE TV Morning Show a ranar Laraba, Daily Trust ta tattaro.
Mista Nwachukwu ya ce sojojin Najeriya sun kasance wata alama ta hadin kan kasa mai sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya dora mata bisa mafi kwarewar aiki daidai da tsarin duniya.
KU KARANTA: Cikakken Bayani: Da Ma Ginin Majalisar Dokoki ta Kasa Na Bukatar Gyara, Lawan
Daily Nigerian ta ruwaito shi yana cewa jami'an soji sun kasance suna bin ka'idojin aiki da kuma kare hakkin dan adam musamman 'yan kasa.
Ya ce:
“Yana da mahimmanci mu tunatar da kanmu cewa wadannan sojojin da ake zarginsu da hadin baki, su ne wadanda a kwanan nan suka sadaukar da rayukansu wajen kwato wadanda aka sace na Makarantar Sakandaren Gwamnati dake Birnin Yawuri daga masu satar mutane.
"Dole ne kuma a nuna, cewa yayin da sojoji ke matukar karbar suka mai ma'ana, bai kamata a tsinkaye su a matsayin wata kofa ta sukar batanci da ke da karfin gwiwa ga masu aikata laifuka ba."
Ya kamata ku zama masu matukar kishin kasa
Kakakin rundunar ya kuma yi gargadin cewa ya kamata a dauki kishin kasa zuwa wani yanayi inda ba kowace magana ne za a ke yi ta batanci game da kasa ba.
Ya kuma umarci shugabannin al'umma da su nuna kishin kasa wajen samar da zaman lafiya, maimakon su zama wakilai wajen yada hargitsi ta hanyar kara ingiza tabarbarewar kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta a yanzu.
KU KARANTA: Duk wanda bai nuna shaidar ya yi NYSC ba kada a dauke shi aiki, DG ya ja kunne
A wani labarin, Shahararren malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi zargin cewa akwai hadin baki tsakanin 'yan fashi da jami'an tsaro.
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Gumi yayi wannan zargin ne a ranar Laraba, 23 ga watan Yuni, yayin wata hira da shi a gidan talabijin na Arise TV.
Gumi ya yi ikirarin cewa 'yan fashi suna samun makaman da jami'an tsaro ke rike da su
Ya yi ikirarin cewa hukumomin tsaro na ba 'yan ta'adda damar mallakar tarin kayan makamai da suke rike da shi.
Malamin ya ce, yanzu haka 'yan bindigar sun dauki satar mutane a matsayin kasuwanci.
Asali: Legit.ng