Mai kamfanin BUA, Abdul Samad Rabi'u ya gwangwaje jihohi 4 da tallafin biliyoyi
- Mai kamfanin kayan abinci na BUA, Abdul Samad Rabiu ya ba da tallafin N10bn ga wasu jihohi
- Tallafin na harkar kiwon lafiya zai kasance ne a tsakanin jihohin Ogun, Kwara, Sokoto da Edo
- Ba wannan ne karo na farko ba, Abdul Samad kan ba da tallafi ga wurare da dama a fadin Najeriya
Kungiyar Abdul Samad Rabiu Africa Initiative (ASR Africa) ta ce za ta bayar da tallafin Naira biliyan 10 don ayyukan kiwon lafiya a jihohi hudu - Ogun, Sokoto, Kwara da Edo.
Ubon Udoh, manajan darakta na ASR Afirka, ya ce za a ba da sabon tallafin ne kan ayyukan kula da lafiya daga kiwon lafiyar mata da yara zuwa kayayyakin kiwon lafiya, bunkasa aiki, da sauransu, The Cable ta ruwaito.
KU KARANTA: Buhari ya sassauta, ya amince zai tattauna da 'yan kudu maso gabas kan rabewa
Wani bangaren jawabin Mista Udoh yana cewa:
"ASR Afirka a yanzu ta yanke shawarar bada N2.5bn ga kowace jiha cikin jihohi hudu a Najeriya - Ogun, Kwara, Sokoto da Edo."
Udoh ya ce kungiyar za ta samar da tsarin yadda za a aiwatar da aikin tare da kungiyoyin aiwatarwa na jiha bayan haka za a raba kashi 50 na tallafin nan take don fara aiwatar da ayyukan.
Ya kara da cewa sauran kaso hamsin za a sake su "daidai da mizanin aikin da aka cimma".
An kafa ASR Afirka a watan Maris na 2021 tare da asusun tallafin shekara-shekara na $100m da aka kebe don warware matsalolin ci gaba a fannonin kiwon lafiya, ilimi da ci gaban zamantakewar Afirka - An ware $50m ga Najeriya sauran kuma ga wasu kasashen Afrika.
Abdul Samad Rabiu ya ba jami'ar Maiduguri tallafin N1bn
Ba wannan ne karo na farko ba, a watan Mayu, ASR Afrika ta ba da tallafin N1bn ga jami'ar Maiduguri dake arewa maso gabashin Najeriya, Punch ta ruwaito.
A nasa jawabin, Shugaban Jami’ar UNIMAID, Farfesa Aliyu Shugaba, ya yaba wa wanda ya kirkiro da shirin, Abdul Samad Rabiu, kan jajircewar da yake yi na kyautatawa al’umma da taimakon al’umma.
KU KARANTA: Badakalar Tinubu: EFCC ta ce tana ci gaba da bincikar shugaban APC Tinubu
Kamfanin MTN Zai Tattara Komai Nashi Ya Fice Daga Najeriya Saboda Wasu Dalilai
A wani labarin, Kamfanin MTN ya yi gargadin yiwuwar dakatar da ayyukansa a Najeriya sakamakon karuwar matsalar rashin tsaro a sassa daban-daban na kasar, TheCable ta ruwaito.
MTN, a wani sako da kamfanin dillacin labarai na Reuters ya gani, ya sanar da kwastomominsa game da yiwuwar jinkiri a hulda dashi.
“Abin takaici, dole ne mu sanar da ku cewa tare da karuwar rashin tsaro a sassa daban-daban na Najeriya; zaku iya samun tseko a sabis dinmu a cikin kwanaki masu zuwa,” kamar yadda aka ruwaito MTN ya ce.
Asali: Legit.ng