Gobara ta janyo asarar miliyoyin naira a gidan kwamishinan 'yan sandan Nigeria

Gobara ta janyo asarar miliyoyin naira a gidan kwamishinan 'yan sandan Nigeria

  • Gobara ta tashi a gidan kwamishinan yan sandan jihar Osun, Olawale Olakode
  • Gobarar wadda ta faru a ranar Lahadi ta yi sanadin asarar dukiyoyin miliyoyin naira
  • Kwamishinan ya mika sako da gwamnan jihar da sauran mutane da suka yi masa jaje

An yi gobara a gidan Olawale Olakode, kwamishinan yan sanda da ke Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, The Cable ta ruwaito.

Gobarar da aka ce ta fara ci a daren ranar Lahadi, misalin karfe 10 da shafe kimanin awanni biyu tana ci.

Taswirar jihar Osun
Taswirar jihar Osun. Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Masu zanga-zangar 'Buhari Must Go' sun banka wuta a hanyar zuwa filin tashin jirage na Abuja

Independent ta ruwaito cewa an yi asarar kaya da dukiyoyi na miliyoyin naira sakamakon gobarar.

Rundunar yan sanda ta tabbatar da afkuwar gobarar

Opala Yemisi, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Osun, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Litinin ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Amma ba a bayyana abin da ya yi sanadin gobarar ba.

Ya ce:

"Gobarar da fara ci misalin karfe 6 na yammacin jiya, 20 ga watan Yunin 2021 ta yi kimanin awanni biyu kafin jami'an hukumar kwana-kwana suka kashe ta.
"Kwamishinan ya yi wa Allah godiya duba da cewa ba a rasa rai ba, sannan ya mika godiya ga dukkan wadanda suka taimaka wurin kashe gobarar a yayin da iyalansa ke lissafa abin da suka yi asara.

KU KARANTA: Mutum 15 cikin waɗanda aka sace a harin Islamiyyar Tegina sun gudo bayan masu tsaronsu sunyi tatil da giya

"Rundunar yan sandan Osun tana mika godiya ga Gwamnan jihar Osun, Mr Gboyega Oyetola, CP Edward Ajogun Awolowo, Area Kwamanda na Abeokuta da dukkan wadanda suka yi wa kwamishinan yan sandan jaje.
"Ofisoshi da dakarun yan sandan jihar Osun suna mika sakon jajensu ga CP da dukkan iyalansa game da abin tausaya da ya same su. Rundunar tana addu'a da fatan Allah ya rubunya masa abin da ya rasa."

A wani labarin, wasu masu zanga-zanga a Umaru Yar'Adua Way, babban birnin tarayya Abuja, a safiyar ranar Litinin sun banka wuta a kan titi, hakan ya janyo cinkoson ababen hawa, Daily Trust ta ruwaito.

Titin na Musa Yar'Adua Way ne ake bi idan za a tafi filin tashi da saukan jiragen sama a birnin tarayyar Abuja.

The Cable ta ruwaito cewa masu zanga-zangar suna ta ihu cewa 'Buhari Must Go' ma'ana 'Dole Buhari Ya Tafi' yayin da suke dauke da takardu masu rubutu daban-daban na nuna rashin kaunar kasancewar shugaban kasar a kan mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel