Da Ɗuminsa: Jirgin Yaƙin NAF Ya Yi Ruwan Bama-Bamai Kan Yan Boko Haram da ISWAP a Borno

Da Ɗuminsa: Jirgin Yaƙin NAF Ya Yi Ruwan Bama-Bamai Kan Yan Boko Haram da ISWAP a Borno

  • Wasu jiragen yaƙin NAF biyu masu saukar angulu sun yi ruwan bama-bamai kan yan ta'addan Boko Haram-ISWAP
  • Rundunar sojin sama ta tabbatar da nasarar harin da jiragen nata suka kai a jihar Borno
  • Kakakin NAF, Edward Gabkwet, yace an hallaka yan ta'addan dama tare da lalata motocin yaƙin su

Jirgin yaƙin rundunar sojin sama (NAF), ya hallaka yan ta'addan Boko Haram-ISWAP, cikinsu harda kwamandojin su a Lamboa, ƙaramar hukumar Kaga, jihar Borno, kamar yadda premium times ta ruwaito.

KARANTA ANAN: El-Rufa'i Ya Yi Kakkausan Gargaɗi Ga Mutanen Dake Toshe Hanyar Kaduna-Abuja

Rahoto ya bayyana cewa jiragen yaƙin NAF masu saukar angulu biyu ne suka yi ruwan bama-bamai kan yan ta'addan, kuma ana tsammanin an kashe sanannen kwamandan ISWAP, Modu Sullum.

Rahoton daily nigerian ya gano cewa gomman mayaƙan ISWAP sun hallaka a yayin harin jiragen yaƙin sojojin sama NAF.

Jirgin yaƙin NAF yayi ruwan bama-bamai kan yan ta'adda
Da Ɗuminsa: Jirgin Yaƙin NAF Ya Yi Ruwan Bama-Bamai Kan Yan Boko Haram da ISWAP a Borno Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Da aka tuntuɓi mai magana da yawun NAF, Edward Gabkwet, ya tabbatar da nasarar da jiragen yaƙin suka samu.

Yace: "Eh, an samu nasara a harin, jiragen yaƙin sun lalata motocin yaƙin yan ta'addan, tare da hallaka adadi mai yawa da mayaƙan."

"A halin yanzu, sojojin ƙasa tare da wasu jami'an mu sun dira wurin domin duba irin nasarar da aka samu."

KARANTA ANAN: Dalilin da Yasa Najeriya Take da Buƙatar Cigaba da Karɓo Bashi, Fashola

An kashe wani babban kwamandan ISWAP

Ana tsammanin harin ya yi sanadiyyar mutuwar wani kwamandan ISWAP, Modu Sulum, wanda ake zargin sa da jagorantar lalata wutar lantarkin Mailanari dake kan hanyar Maiduguri-Damaturu.

Hakanan kuma, ana zargin Solum da kitsa hare-haren da ake kaiwa matafiya a kan hanyar Auno-Jakana.

A wani labarin kuma Shugaba Buhari Ya Buƙaci Kamfanin MTN Ya Rage Farashin 'Data' Ga Yan Najeriya

Shugaba Buhari ya roƙi kamfanin sadarwa na MTN ya sauƙaƙa wa yan Najeriya masu amfani da layukan su, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Buhari yace Najeriya ce ƙasa ta uku a duniya da kamfanin ya fi samun kuɗaɗen shiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel