El-Rufa'i Ya Yi Kakkausan Gargaɗi Ga Mutanen Dake Toshe Hanyar Kaduna-Abuja

El-Rufa'i Ya Yi Kakkausan Gargaɗi Ga Mutanen Dake Toshe Hanyar Kaduna-Abuja

  • Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i ya gargaɗi mutanen jihar sa a kan toshe hanyar Kaduna-Abuja
  • Gwamnan yayi wannan gargaɗi ne yayin ziyarar ta'aziyya da yakai yankunan, inda ya tattauna da mutanen yankunan
  • Yace toshe hanya ba zai haifar da wani sakamako mai kyau ba, sai takura wa matafiya

Gwamna Malam Nasiru El-Rufa'i na jihar Kaduna, ya kai ziyarar ta'aziyya ga ƙauyukan dake kan hanyar Kaduna-Abuja, waɗanda harin yan bindiga ya shafa, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Gwamnan wanda ya samu rakiyar kakakin majalisar dokokin Kaduna, Rt. Hon. Yusuf Ibrahim Zailani, ya ziyarci Sabon Gayan da Kakkau kuma ya zanta da mutanen yankunan, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Dalilin da Yasa Najeriya Take da Buƙatar Cigaba da Karɓo Bashi, Fashola

El-Rufa'i yayi ta'aziyya ga mutanen ƙauyukan da sauran garuruwan da irin wannan lamarin ya shafa a faɗin jihar.

Ya kuma ƙara tabbatar da ƙoƙarin gwamnatinsa na shawo kan matsalar tsaron jihar musamman kare rayuwar al'umma da dukiyoyinsu.

El-Rufai ya gargaɗi masu toshe hanyar Kaduna-Abuja
El-Rufa'i Ya Yi Kakkausan Gargaɗi Ga Mutanen Dake Toshe Hanyar Kaduna-Abuja Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Yace: "Gwamnatin mu na aiki ba dare ba rana tare da hukumomin tsaro domin tabbatar da kare rayukan mutane da dukiyoyin su."

"Ina gargaɗin ku kan toshe hanya, wannan ba dai-dai bane kuma yana taɓa rayuwar waɗanda ba su ji ba basu gani ba, domin hakan na tilasta wa matafiyan da suka biyo hanyar tsayawa."

Gwamnatin Kaduna ta bayyana ƙauyukan da aka kai hari makon da ya gabata

A wani jawabi da kwamishinan tsaro na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya fitar ya bayyana ƙauyukan da yan ta'adda suka kai hari daga ranar Litinin 14 ga watan Yuni zuwa Jumu'a 18 ga watan Yuni

Kwamishinan ya kara da cewa a dukkan hare-haren da yan bindiga suka kai waɗannan yankuna sai an samu rahoton kashe wasu.

KARANTA ANAN: PDP Ta Ragargaji APC a Zaɓen Cike Gurbin da Aka Gudanar a Jihar Kaduna

Yankunan sun haɗa da; Kakkau, Damba-Kasaya, Kankomi, Kajuru, Idasu, Karaukarau, da Sobawa a ƙarkashin kananan hukumomin Giwa da Kajuru.

"Gwamna Malam Nasiru El-Rufa'i na miƙa saƙon ta'aziyya ga dukkan iyalan da harin yan bindigan ya shafa," inji Aruwan.

A wani labarin kuma Mu Haɗu a Filin Yaƙi, Gwamna Yayi Alƙawarin Shiga Daji Domin Yaƙi da Yan Bindiga

Gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu, yayi alƙawarin shiga cikin daji domin yaƙi da yan bindiga a jiharsa, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Bagudu yace addini ya amince a sadaukar da rayuwa domin kare martaba, dukiya da imani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel