Minista Ya Bayyana Yadda ’Yan Najeriya Ke Kokarin Tura Buhari Ga Halaka

Minista Ya Bayyana Yadda ’Yan Najeriya Ke Kokarin Tura Buhari Ga Halaka

  • Ministan Kwadago ya bayyana yadda 'yan Najeriya ke tunzura shugaba Buhari duk da yawan hakurinsa
  • Ya ce Buhari ya jure suka da yawa daga 'yan adawa, kuma ba kowane shugaba bane zai aminta da hakan
  • Hakazalika Ngige ya bayyana amincewarsa ga ba jama'ar kudu maso gabas kujarar shugaban kasa a 2023

Ministan kwadago da samar da ayyukan yi Dakta Chris Ngige ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya jure da yawa daga masu sukarsa, yana mai sake jaddada cewa ‘yan Najeriya da dama na son kure shi (Buhari) fiye da yadda ya kamata.

Ngige ya yi magana ne lokacin wata tattaunawa da Channels Tv a cikin shirin News Night wanda aka watsa a ranar Litinin kuma Legit.ng Hausa ta samo, inda ya bayyana cewa shugabanni da yawa ba za su amince da irin sukar da Buhari ke fuskanta ba.

"Shin Shugaba Obasanjo zai iya baku damar irin wannan hali?… Ba zai bar ku haka ba! Don haka, wannan shugaban (Buhari) doki ne mai gudun tsiratarwa amma ku (‘yan Najeriya) kuna son ingiza shi ya mutu,” in ji Ngige yayin tattaunawar.

KU KARANTA: Gwamna Ganduje ya magantu kan batun yin ritayarsa daga siyasa

Minista ya bayyana yadda 'yan adawa ke kokarin kure hakurin shugaba Buhari
Chris Ngige, Ministan Kwadago na Najeriya | Hoto: icirnigeria.org
Asali: UGC

Tsohon gwamnan na jihar Anambra yayin da yake jaddada cewa gwamnati mai ci a yanzu ta cika alkawurranta a fannoni da dama, ya yi kira ga masu sukar da sauran jama'a da su yi wa gwamnatin Buhari fatan alheri.

“Dole ne a samu iyaka ga siyasa. Idan gwamnati ta yi kyau, idan mutum ya yi abin kirki, a yaba mishi. A wuraren da bai yi rawar gani ba, nuna mishi ya gyara,” ya kara da cewa.

Ngige ya bayyana amincewarsa a ba jama'ar kudu maso gabas shugabanci a 2023

Kiraye-kirayen neman ba da kujerar shugaban kasa zuwa yankin kudu maso gabas sun yi yawa kuma an samu rarrabuwar kawuna a cikin kasar da ta fi yawan al'umma a Afirka, wato Najeriya.

Amma Ngige ya amince da wadanda ke ganin ya kamata zaben 2023 ya zama an tura kujerar ta shugaban kasa zuwa kudu, musamman Ibo.

Ngige ya yi imanin cewa za a magance rikice-rikicen da ke kudu maso gabas idan shugabancin kasar ya kasance a hannun dan kabilar Ibo.

“Don haka na yarda da waccar shawara, duk da cewa, kundin tsarin mulkin Najeriya bai zo da shi ba. Anan ne nake kalubalantar wadanda suka rubuta Kundin Tsarin Mulki na 1999.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari za ta gurgunta Najeriya, PDP ta koka kan yawan cin bashi

A wani labarin daban, Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya ce Najeriya na bukatar karin shugabanni masu kwazo da shirye-shiryen hada kan kasar, Punch ta ruwaito.

Ya fadi haka ne a Legas a ranar Lahadi yayin wata ziyarar ban girma a fadar Oniru na Iruland, Oba Abdulwasiu Omogbolahan Lawal, a yayin bikin murnar nadin sarauta karo na farko.

Ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa mai taken, ‘Najeriya na bukatar shugabannin da suke shirye domin hada kan 'yan Najeriya, in ji Osinbajo a wajen bikin cika shekara daya da nadin sarautar Oniru ’, wacce hadiminsa na yada labarai, Laolu Akande ya fitar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.