Mu Tagwaye Ne: Koriya Ta Arewa Na Bukatar Kara Dankon Alaka da Najeriya
- Gwamnan kasar Koriya ta Arewa ta bayyana bukatar bunkasa alaka tsakaninta da Najeriya
- Gwamnatin kasar ta ce Najeriya Koriya ta Arewa suna da manufofi iri daya, kuma akwai alaka
- Kasar Koriya ta Arewa da Najeriya sun jima suna kawance tare da alaka mai karfin gaske
Jakadan Koriya ta Arewa a Najeriya Chi Tun Chon Hu, ya ce gwamnatinsu ta ba da fifiko wajen bunkasa alakar kasashen biyu, BBC ta ruwaito.
Ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Abuja lokacin da ya ziyarci Shugaban Jam’iyyar APC na kasa.
Ya ce ya lura cewa Najeriya da Koriya ta Arewa sun yi tarayya a abu daya, inda ya ce rajistar jam’iyya da jam’iyya mai mulki a kasar ta APC ta yi a kwanan nan babbar nasara ce.
KU KARANTA: Me Ya Rage Nake Nema: Masari Ya Ce Daga 2023 Zai Yi Sallama da Siyasa
Jakadan ya ce: “Kasashenmu biyu suna da dadaddiyar dangantaka da hadin kai.musamman ta fuskar kirkire-kirkire da ke amfanar kasashen biyu.
A shekarun baya cikin shekarar 2018, shugaban kasar Koriya ta Arewa, ya yi alkawarin hada karfi da karfe da Najeriya don samar da dawwamammen zaman lafiya da tsaro, kamar yadda jakadan kasar a Najeriya na wancan lokacin, Jong Yong Chol ya bayyana.
Majiyar Legit ta ruwaito jakadan cewa ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ya fitar a yayin bikin cikar tsohon Shugaban kasar Kim Jong-II, cika shekaru 76, da ace yana raye, a babban birnin tarayya Abuja.
KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: Najeriya Za Ta Buga Wa Kasar Gambia Kudade, Ba Sauran Kai Wa Turai
A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata ya ce dole ne kasashen Afirka ta Yamma da ke fama da rikice-rikice su hada karfi da karfe don ceto yankin daga ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP, PM News ta ruwaito.
Shugaban ya yi magana ne a Fadar Shugaban Kasa dake Abuja, yayin karbar sabon Wakilin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya na Yammacin Afirka da yankin Sahel (UNOWAS), Mista Mahamat Saleh Annadif, dan kasar Chadi.
Buhari ya ce: “Kai ne makwabcinmu. Kana da kwarewa sosai kan al'amuran da suka shafi yankin Sahel, ka yi shekaru biyar a Mali. Ina fatan za ka sa kasashen su yi aiki tare don tunkarar matsalolin da suka shafe su."
Asali: Legit.ng