An Kame Buhunnan Kudi da Aka Shigo Dasu Daga Kasar Waje a Filin Jirgin Jihar Kano
- Jami'an tsaron Najeriya sun kame wasu kudade da wani jirgi ya shigo dasu Najeriya, jihar Kano
- Hukumar EFCC ta tattara kudaden zuwa ofishinta, bayan da jami'an tsaro suka mamaye wurin kudin
- Sai dai, mai magana da yawun hukumar EFCC bai tabbatar da faruwar lamarin ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton
Jami'an hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS), da ke aiki a Filin jirgin saman Malam Aminu Kano (MAKIA), a ranar Alhamis sun bankado wasu manya-manyan buhunna da aka makare da kudaden kasashen waje wanda jirgin saman Habasha ya shigo da su.
Wasu majiyoyin tsaro a filin jirgin da suka nemi a sakaya sunanayensu sun bayyana wa Daily Nigerian cewa an gano kudaden ne da aka lullube su a cikin wasu manya-manyan buhunna guda uku, bayan da jirgin ya sauke kayan ya tashi da misalin karfe 2 na dare.
Majiyar ta kara da cewa jami’an da ke bakin aiki, wadanda suka hada da jami'an tsaro na jirgin sama, Kwastam da jami’an SSS ba tare da bata lokaci ba suka sanar da jami’an hukumar EFCC wadanda suka iso wurin kuma suka kwashe kudaden.
KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: Buhari Ya Isa Borno, Ya Bukaci Sojoji Su Kara Daura Damara
Majiyar ta ce:
“Kwatsam sai muka ga isowar jami’an tsaro dauke da makamai ciki har da 'yan sanda, jami’an Kwastam, jami’an EFCC da sauransu.
“Lokacin da suka iso, sai suka killace yankin suka fara kwashe buhunan kudin daga tashar.
“Jami’an EFCC sun zo da na’urar kirga kudi sun fara kirga kudin daga misalin karfe 2 na dare har zuwa misalin karfe 6 na yamma."
Mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren, ya ce ba a yi masa bayani game da lamarin ba, amma ya ce zai kira ofishin na Kano don tabbatar da labarin.
Bawa Ya Bayyana Yadda EFCC Zata Bankado Wadanda Ke Hana Najeriya Ci Gaba
Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, ya ce hukumar za ta bakado wadanda ke dakile ci gaban Najeriya, TheCable ta ruwaito.
Da yake jawabi a taron manema labarai na gidan gwamnatin da aka yi a Abuja ranar Alhamis, Bawa ya ce EFCC ta dukufa wajen tabbatar da cewa Najeriya ta kubuta daga dukkan nau'ikan laifuka da suka shafi kudi da tattalin arziki.
Ya ce hukumar na da
“kwarin gwiwar ma’aikata da goyon baya daga kowane mai ruwa da tsaki a cikin gida da waje don cimma manufar Najeriya na zama ba tare da aikata nau’ikan laifukan tattalin arziki da na kudi ba”.
“Najeriya ce kadai kasar da muke da ita. Mu ne wadanda za mu kiyaye ta kuma ba shakka, muna bukatar goyon bayan wadanda suke gida da kuma kasashen waje.”
"Don Allah kar ku tsallaka layin nan kuma ku tuna cewa idan ba ku tare damu mu a kokarin kai Najeriya tudun na tsira, EFCC za ta bankado ku a ko'ina, kowane lokaci."
KU KARANTA: 'Yan Sanda Sun Shiga Shagali Bayan Da ’Yar Sanda Ta Haifi Jarirai ’Yan Uku
Badakala: Shugaban EFCC Ya Ci Alwashin Gurfanar da Wani Babba a Jami'iyyar APC
A wani labarin, Shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya sha alwashin cewa hukumar za ta sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Kalu.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Bawa ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja a ranar Alhamis, 17 ga watan Yuni.
Kalu, wanda yanzu haka dan majalisar dattijai ne, Kotun Koli ta sake shi a kan ka'idoji bayan an same shi da laifin satar biliyoyin nairori lokacin da yake gwamnan jihar Abia tsakanin 1999-2007.
Asali: Legit.ng