Alhaji Ibrahim Mohammed: Ku sadu da Sarkin makafi a Ibadan wanda ke da mata 3 da yara da yawa
- Mabarata a Ibadan, jihar Oyo, sun koma yankin Akinyele a ranar Talata, 15 ga Yuni
- Alhaji Ibrahim Mohammed, wanda shine 'sarkin makafi', ya ba da labarin halin da ya tsinci kansa bayan zama a yankin na ‘yan kwanaki
- Mohammed ya godewa Gwamna Makinde kan samar da sabon matsugunin sannan kuma ya bukace shi da ya yi masu karin aiki
Kwanaki bayan Gwamna Seyi Makinde ya ba da umarnin kwashe mabarata daga yankin Sabo da ke Ibadan zuwa sabuwar cibiyar da aka gina a Akinyele, Alhaji Ibrahim Mohammed, wanda aka bayyana a matsayin 'sarkin' makafi a jihar Oyo, ya yi magana game da sabon gidan.
A wata hira ta musamman da jaridar Nigerian Tribune, Alhaji Mohammed wanda ke da mata uku da ‘ya‘ya masu yawa ya nuna godiya ga Gwamna Makinde game da wannan abin da ya yi.
KU KARANTA KUMA: Dubi jerin birane 10 mafi wahalar zama a duniya a shekarar 2021
Bayan nan, ya kuma bayyana wasu mahimman damuwa waɗanda yake son gwamnan Oyo ya magance.
Sabon matsugunin ya fi mazaunin Sabo
Alhaji Mohammed ya ce yana matukar farin ciki da sabon wurin, ya kara da cewa mutanensa suna matukar godiya ga Gwamna Makinde.
Kalaman nasa:
"Wannan wurin yana da kyau kuma yafi dama-dama, idan aka kwatanta da inda muke zaune a baya. Yana da kayan aiki waɗanda suka sauƙaƙa mana rayuwa. Muna godiya da alherin da gwamnan ya nuna."
Sabon wurin, a cewarsa, yana da ruwa daga rijiyoyin burtsatse, cibiyar kiwon lafiya, bandakuna da lantarki mai amfani da hasken rana.
Alhaji Mohammed ya ce, gwamnatin jihar tana daukar nauyin ciyar da mabarata sama da 3,000 a cibiyar.
Makinde ya yi mana kokari amma muna son karin abubuwa
Da mata uku da yara da yawa, Alhaji Mohammed ya bukaci Gwamna Makinde da ya gina masa da sauran mazaje masu mata fiye da daya dakuna daban-daban a cibiyar.
Ya ce:
"A matsayina na mai aure, bai dace da ni ba in kwana a daki daya tare da dukka matana.
"Don haka, ina rokon mai girma gwamna da ya taimaka ya gina mana dakuna saboda ma'aurata a tsakaninmu."
KU KARANTA KUMA: Sace dalibai: Mun samu labarin shige da ficen ‘yan bindiga kafin harin makarantar Yauri – Gwamna Bagudu
Makaranta da wutar lantarki
Duk da cewa an samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana, Alhaji Mohammed yana son a hada sabuwar cibiyar da wuraren samar da wutar lantarki na jama'a don zama wata mafita ta daban.
Ya kuma bukaci gwamnatin jihar da ta gina makaranta a cibiyar saboda yaran.
Gwamna Ya Ba da Umarnin a Kwashe Mabarata Zuwa Wurin Alfarma a Jiharsa
A baya mun ji cewa Gwamnatin jihar Oyo ta fara aikin kwashe mabarata daga lungunan Jemibewon, yankin Mokola-Sabo na Ibadan zuwa sabuwar cibiyar sake matsuguni na Akinyele da aka gina a cikin garin.
Wakilin Legit.ng da ke Ibadan, Ridwan Kolawole, ya ruwaito cewa cibiyar sake matsugunin da ta fara watannin baya, an bude ta ne da sanyin safiyar Talata, 15 ga Yuni.
Wannan ya biyo bayan rangadin sabon wajen ne da shugabannin al’ummar Arewa da wakilan mabaratan suka yi a ranar Asabar, 12 ga Yuni.
Asali: Legit.ng