Gwamna Ya Ba da Umarnin a Kwashe Mabarata Zuwa Wurin Alfarma a Jiharsa

Gwamna Ya Ba da Umarnin a Kwashe Mabarata Zuwa Wurin Alfarma a Jiharsa

  • An kwashe mabarata a jihar Oyo daga mashahurin yankin Mokola na Ibadan zuwa cibiyar sake matsuguni na Akinyele
  • Taiwo Adisa, babban sakataren labarai na gwamna Makinde, shine ya bayyana hakan a garin Ibadan a ranar Talata, 15 ga watan Yuni
  • Adisa ya lura cewa sabon matsugunin an wadata shi da abubuwan more rayuwa ciki har da asibitoci da wuraren shakatawa

Gwamnatin jihar Oyo ta fara aikin kwashe mabarata daga lungunan Jemibewon, yankin Mokola-Sabo na Ibadan zuwa sabuwar cibiyar sake matsuguni na Akinyele da aka gina a cikin garin.

Wakilin Legit.ng da ke Ibadan, Ridwan Kolawole, ya ruwaito cewa cibiyar sake matsugunin da ta fara watannin baya, an bude ta ne da sanyin safiyar Talata, 15 ga Yuni.

Wannan ya biyo bayan rangadin sabon wajen ne da shugabannin al’ummar Arewa da wakilan mabaratan suka yi a ranar Asabar, 12 ga Yuni.

KU KARANTA: Osinbajo ya siffanta irin shugabannin da Najeriya ke bukata a kowane bangare

Da dumi-dumi: Gwamna ya ba da umarnin a tattara mabara fadin jiharsa
Wasu daga cikin mabarata dake bara a bakin titi | Hoto: ghbase.com
Asali: UGC

Taiwo Adisa, babban sakataren labarai na gwamna Seyi Makinde, ya bayyana cewa kwamishinan muhalli na jihar, Idowu Oyeleke, ya jagoranci rukunin farko na wadanda aka kwashe zuwa matsugunin na Akinyele.

Oyeleke ya ce wannan sabon matsuguni yana dauke da kayayyakin more rayuwa wadanda suka hada da makarantu, asibitoci, da kuma wuraren shakatawa.

A cewar Adisa, sauran ma’aikatun da abin ya shafa sun hada da lamuran mata da hada kan jama’a, bayanai, al’adu da yawon bude ido da lamuran cikin gida da na sarauta.

Ofishin babban sakatare, Asusun Tsaro na Jihar Oyo, karkashin jagorancin Fatai Owoseni, wanda kuma shi ne mai ba da shawara na musamman kan harkokin tsaro ga gwamnan an ambaci sunansa a matsayin wani bangare na aikin.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari za ta gurgunta Najeriya, PDP ta koka kan yawan cin bashi

A wani labarin, Wasu da ake zargin makiyaya ne sun yanke hannun dama na wani manomin shinkafa mai suna Saheed Zakariyau, a kauyen Bindofu dake masarautar Lafiagi, a karamar hukumar Edu ta jihar Kwara, Punch ta ruwaito.

Manomin, a cewar majiyoyi, ana zargin an kai masa hari ne a gonarsa da ke kauyen Bindofu a ranar Asabar da ta gabata bayan ya zargi makiyayan da ingiza dabbobinsu wajen lalata gonarsa.

An tattaro cewa wanda manomin, tare da abokan aikinsa, ya je gonar a ranar Asabar kuma ya gano cewa makiyayan sun yi kiwon shanunsu a gonarsa tare da lalata amfanin gonar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel