Yanzu-Yanzu: Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari Ya Dira Maiduguri

Yanzu-Yanzu: Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari Ya Dira Maiduguri

  • Shugaba Buhari, ya dira Maiduguri, babban birnin jihar Borno, a wata ziyarar kwana ɗaya da yakai jihar
  • An sa ran shugaban zai jagoranci buɗe sabbin gidaje 10,000 da gwamnatinsa ta gina wa yan gudun hijira
  • Gwamnan jihar Borno, Babagana Umaru Zulum, tare da shugabannin jami'an tsaro, sune suka tarbi shugaban a filin jirgi

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya dira Maiduguri, jihar Borno, a wata ziyarar aiki ta kwana ɗaya da ya kai jihar.

Shugaba Buhari, wanda jirginsa ya dira a filin jirgin ƙasa-da-ƙasa dake Maiduguri da misalin karfe 9:45 na safe, ya samu rakiyar manyan jami'an gwamnatinsa.

KARANTA ANAN: Shugabannin Tsaro CDS, COAS, CAS, da IGP Sun Dira Maiduguri Gabanin Zuwan Shugaba Buhari

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, tare da dukan shugabannin jami'n tsaro ƙasar nan ne suka tarbi shugaba Buhari ranar Alhamis.

Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, ya dira Maiduguri
Yanzu-Yanzu: Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari Ya Dira Maiduguri Hoto: Buhari Sallau FB Fage
Asali: Facebook

Buhari zai ƙaddamar da gidaje 10,000 da gwamnatinsa ta gina wa yan gudun hijira

A yayin ziyarar, Shugaba Buhari zai ƙaddamar da sabbin gidaje 10,000 da gwamnatinsa ta ginawa yan gudun hijira, waɗanda rikicin Boko Haram ya shafa.

Wannn na ƙunshe ne a wani rubutu da mai taimkawa shugaban ta ɓangaren labarai, Bashir Ahmad, ya fitar a shafinsa na Facebook.

KARANTA ANAN: Ma'aikata 774,000: Dubbannin Ma'aikatan SPW Sun Koka Ga FG Kan Rashin Biyansu Haƙkoƙinsu

Yace: "Yayin zamansa a Maiduguri, shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, zai jagoranci buɗe sabbin gidaje 10,000 da gwamnatinsa ta gina wa yan gudun hijira."

Gidajen guda 10,000 da za'a ƙadɗamar sune rukuni na farko da gwamnati ta gina wa al'ummar jihar Borno, waɗanda rikicin Boko Haram ya raba su da muhallinsu.

Buhari a Maiduguri
Yanzu-Yanzu: Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari Ya Dira Maiduguri Hoto: Buhari Sallau FB Fage
Asali: Facebook

Legit.ng hausa ta tattaro muku wasu daga cikin ra'ayoyin yan Najeriya a kan ziyarar da shugaban yakai Borno.

Alh Modu Ali, yace:

"A shirye muke mu tarbi wannan babban baƙo, shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, kwamnandan rundunar jami'an tsaro ta Najeriya."

Mustapha Naiya Gaya, yace:

"Wannan babban nasara ce ga shugaba Buhari, Masha Allah! Allah yasa a kammala lafiya."

Nuraddeen Abdulrasheed, yace:

"Muna wa shugaba Buhari da yan tawagarsa addu'ar Allah ya dawo mana da su cikin aminci."

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Mai Horad Da Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa

Yan bindiga sun sace mai horad da tawagar yan wasan kwallon ƙafa ta Rivers United, Stanley Eguma.

Wata majiya dake kusa da hukumar shirya wasanni ta ƙasa NPFL ta tabbatar da faruwar lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262