An kame wani Fasto da ya kashe matarsa, ya binne gawar a kusa da cocinsa

An kame wani Fasto da ya kashe matarsa, ya binne gawar a kusa da cocinsa

  • Bayan kashe matarsa da binne ta na kwanaki bakwai, an kame Faston da ya aikata mummunan aikin
  • Rahotanni sun bayyana cewa, husuma ta hada Fasto da matarsa, lamarin da ya kai ga har ya kashe ta
  • Majiyoyi sun bayyana yadda lamarin ya faru, kuma Faston ya amsa laifinsa ba tare da tursasawa ba

‘Yan sanda sun kame wani fasto a jihar Akwa Ibom yankin Kudu maso kudancin Najeriya bisa zargin kashe matarsa.

Lamarin ya faru ne a wani kauye da ake kira Ikot Ataku, Okon, a karamar hukumar Eket. An bayyana faston a matsayin Chris Enoch, wanda ya kafa cocin Omega Word Global Ministries.

Ya fito ne daga jihar Ebonyi a yankin Kudu maso gabashin Najeriya..

Shugaban matasa na Okon Clan, Effiong Johnson ya fada wa Premium Times a daren Laraba, cewa Mista Enoch ya kashe matar, Patience, kwanaki bakwai da suka gabata kuma ya binne gawarta a cikin wani rami mara zurfi a cikin gidan da suke ciki

KU KARANTA: 'Yan Sanda Sun Shiga Shagali Bayan Da ’Yar Sanda Ta Haifi Jarirai ’Yan Uku

An kame wani da Fasto ya kashe matarsa, ya binne gawar a cikin rami mara zurfi
Ramin da Faston ya binne matarsa bayan ya kashe ta | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ya kuma ce Faston na da ’ya’ya biyar. Babban yaron yana da shekaru 15.

Legit ta tattaro cewa, cocin na Mr Enoch yana hade da katafaren gidan da yake haya, inda ya binne matar.

Al’ummar yankin sun shiga shakku lokacin da yaran Faston suka kai kararsa ga makwabta cewa ba su ga mahaifiyarsu ba kwanaki bayan ta yi fada da mahaifinsu.

Matasan yankin, karkashin jagorancin shugabansu, Mista Johnson, wanda kuma ‘jami’in ’yan sandan yankin ne, sun je bincikar gidan Faston kuma sun yi mamakin gano gawar matar da ya binne a cikin wani rami mara zurfi. Matasan sun mika Faston ga ‘yan sanda.

Baki shi ke yanka wuya: Faston ya amsa laifin cewa shi ya kashe matarsa da hannunsa

Matar da aka kashe karamar 'yar kasuwa ce da ke sayar da kek a kasuwar yankin.

"Yanzu tahowa ta daga ofishin 'yan sanda, ya budi baki cewa ya kashe matar kimanin kwanaki bakwai da suka gabata," in ji Mista Johnson.

“Daga abin da yaran suka ce, su (Faston da matar) sun kasance suna samun matsala kuma wani lokacin yakan ce a gaban yaran cewa zai kashe matar kuma ba abin da zai faru.

Ya kara da cewa "A wannan rana musamman, mutumin ya kori yaran lokacin da shi da matar suka fara fada."

Shugaban Okon Clan, Akpabio Inyang, ya ziyarci inda lamarin ya faru.

Lokacin da aka tuntube shi, Jami'in 'Yan sanda na Shiyya a Eket, Sunday Digha, ya ki cewa komai kan lamarin.

Ya ce mai rahoton ya yi magana da kakakin 'yan sanda a jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sanda, Odiko MacDon, ba ta amsa kiran waya ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta zargi gwamnonin PDP da kin kawo karshen rikicin makiyaya

A wani labarin, Wasu da ake zargin makiyaya ne sun yanke hannun dama na wani manomin shinkafa mai suna Saheed Zakariyau, a kauyen Bindofu dake masarautar Lafiagi, a karamar hukumar Edu ta jihar Kwara, Punch ta ruwaito.

Manomin, a cewar majiyoyi, ana zargin an kai masa hari ne a gonarsa da ke kauyen Bindofu a ranar Asabar da ta gabata bayan ya zargi makiyayan da ingiza dabbobinsu wajen lalata gonarsa.

An tattaro cewa wanda manomin, tare da abokan aikinsa, ya je gonar a ranar Asabar kuma ya gano cewa makiyayan sun yi kiwon shanunsu a gonarsa tare da lalata amfanin gonar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel