'Yan Sanda Sun Shiga Shagali Bayan Da ’Yar Sanda Ta Haifi Jarirai ’Yan Uku

'Yan Sanda Sun Shiga Shagali Bayan Da ’Yar Sanda Ta Haifi Jarirai ’Yan Uku

  • Abin farin ciki ya lullube iayalan wata mata mai aiki a hukumar 'yan sanda ta jihar Ogun
  • An ruwaito cewa, matar ta haifi jarirai uku lafiyayyu, lamarin da ya sanya jama'a farin ciki
  • Hukumar ta 'yan sanda ta garzaya domin ganewa idanunta wannan babbar kyauta da aka samu

Wata ‘yar sanda da ke aiki a rundunar ‘yan sanda ta Jihar Ogun, Bolaji Senjirin ta haifi 'yan uku - maza biyu da mace daya, Daily Trust ta ruwaito.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Edward Ajogun, ya ziyarci dangin a yankin Kemta na garin Abeokuta a ranar Laraba tare da mambobin kwamitin hulda da jama'a na 'yan sanda (PCRC).

Ajogun ya nuna godiya ga Allah Madaukakin Sarki bisa yadda ya ba su kyautar jariran lafiya, yana mai bai wa dangin tabbacin ci gaba da ba su kulawa.

KU KARANTA: Mai Jiran Gadon Sarauta Ya Yanke Jiki Ya Fadi Matacce a Wajen Tantance Shi

Farin ciki: Jami'ar 'yar sanda ta haifi jarirai 'yan uku a jihar Ogun
Jariri sabon haihuwa | Hoto: bbc.co.uk
Asali: UGC

Mahaifiyar mai shayar da ‘yan uku ta kasance dogariya ga matar kwamishina Ajogun.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda (PPRO), Abimbola Oyeyemi a cikin wata sanarwa ya ce kwamishinan 'yan sandan ya ba da gudummawar kudi ga jariran tare da yin addu'ar zasu rayu don cika burinsu.

Hakazalika, shugaban PCRC a jihar, Arch. Samson Kunle Popoola ya sanar da bayar da gudummawar kudi na N25,000 a madadin kungiyar yayin da reshen mata shi ma ya yi alkawarin tallafa wa dangin.

Sauran jami'an da ke tare da Ajogun sun hada da sashen DPO na Kemta, CSP Grace Ejiofor da kuma mataimakin Ajogun na musamman, DSP Ade Ekiti.

KU KARANTA: Mai Jiran Gadon Sarauta Ya Yanke Jiki Ya Fadi Matacce a Wajen Tantance Shi

Wata mata ta haifi yara 10 a lokaci guda, ta karya tarihin duniya

A wani labarin, Gosiame Thamara Sithole mai shekaru talatin da bakwai ta haifi yara jarirai goma a daren Litinin, 7 ga Yuni; Mahaifiyar ta yi tsammanin za ta haifi yara takwas kamar yadda aka nuna a lokacin haihuwa amma an sake samun ƙarin jarirai biyu yayin haihuwar.

A cewar wani rahoto da Pretoria News da wasu kafafen yada labarai suka fitar, Thamara ta haifi yaranta maza bakwai da mata uku ta hanyar fida a cikin asibitin Pretoria.

Yanzu ta zama uwa mai yara 12 tunda dama tanada tagwaye ‘yan shekaru shida. A cewar mijinta, Teboho Tsotetsi, cikin matar gaba kyauta ce daga Allah domin ba ta taba shan kowane irin maganin haihuwa ba.

A wata hira da aka yi da ita wata daya da ta gabata kafin ta haihu, mahaifiyar mai yara 12 a yanzu ta ce ta kadu matuka lokacin da aka sanar da ita cewa zata haifi yara da yawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.