Ma'aikata 774,000: Dubbannin Ma'aikatan SPW Sun Koka Ga FG Kan Rashin Biyansu Haƙkoƙinsu

Ma'aikata 774,000: Dubbannin Ma'aikatan SPW Sun Koka Ga FG Kan Rashin Biyansu Haƙkoƙinsu

  • Har yanzun gwamnatin tarayya bata biya mafi yawancin ma'aikatan SPW hakƙokin su ba
  • Rahotanni sun bayyana cewa an biya wasu kuɗin wata ɗaya yayin da wasu ko sisi ba'a biya su ba
  • A shekarar da ta gabata ne, shugaba Buhari ya amince da ɗaukar yan Najeriya marasa aikin yi 774,000 a faɗin Najeriya

Dubbannin ma'aikatan da gwamnatin tarayya ta ɗauka a shirin SPW sun koka kan rashin biyan su Naira N20,000 na tsawon watanni uku, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Rahoto ya bayyana cewa har yanzun mafi yawancin waɗanda aka ɗauka a tsarin aikin SPW na tsawon wata uku (Fabrairu-Afrilu) ba'a biya su N20,000 kamar yadda aka musu alƙawari ba.

KARANTA ANAN: Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Mai Horad Da Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa

A jihar Borno, wasu ma'aikatan sun ce sau ɗaya kacal aka biya su hakkinsu na Naira N20,000

Hajja Fanna, daga garin Gamboru, ƙaramar hukumar Ngala, tace har yanzun tana jiran ragowar kuɗinta N40,000 na watanni 2.

Dubbannin Ma'aikatan SPW Sun Koka Ga FG Kan Rashin Biyansu Haƙkoƙinsu
Ma'aikata 774,000: Dubbannin Ma'aikatan SPW Sun Koka Ga FG Kan Rashin Biyansu Haƙkoƙinsu Hoto: specialpublicworks.gov.ng
Asali: UGC

Wani mutumi daga ƙaramar hukumar Jere, wanda ya nemi a sakaya sunan shi, yace yayi aiki a tsarin amma har yanzun ba'a biya shi ko sisi ba.

Shugabar NDE ta jihar Borno tace ya kamata ace kowa ya samu N20,000 duk wata

Shugaban NDE reshen jihar Borno, Mrs Mairo Aliyu, tace an ɗauki marasa aikin yi 1,000 daga kowace ƙaramar hukuma 27 da ake da su a Borno.

Ta kuma tabbatar da cewa ya kamata ace dukan ma'aikatan an biya su N20,000 har na tsawon wata uku, duk kuwa da cewa watannin da aka ware domin aikin sun wuce.

Ta bayyana cewa matsalolin daga banki ne, inda wasu bankunan suka bada uzurin su amma suna kan aikin biyan ma'aikatan.

Ma'aikatan Kaduna sun koka kan rashin biyan su haƙƙin su

A jihar Kaduna, bincike ya nuna cewa da yawan ma'aikatan da aka ɗauka a shirin SPW basu samu kuɗaɗen su ba.

Ɗaya daga cikin ma'aikatan, Jibril, daga ƙaramar hukumar Kaduna ta arewa, yace har yanzun ba'a biya shi ko sisi ba.

Yace: "Mafi yawancin mu daga ƙaramar hukumar Kaduna ta arewa ba'a bamu hakkinmu ba kuma ba mu san dalili ba saboda an kammala aikin tun watan Afrilu."

KARANTA ANAN: Shugabannin Tsaro CDS, COAS, CAS, da IGP Sun Dira Maiduguri Gabanin Zuwan Shugaba Buhari

Shugaba Buhari ya amince da ɗaukara ma'aikata 774,000 a tsarin SPW

A shekarar da ta gabata, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da ɗaukar ma'aikata 1,000 daga kowace ƙaramar hukuma 774 da ake da su a Najeriya.

FG tace tsarin zai ƙunshi mutanen da basu da aikin yi kuma ba su da ƙwarewar sana'a daga ƙananan hukumomi 774.

Sai-dai waɗanda aka ɗauka a tsarin, zasu gudanar da wasu ayyukan gyara a yankunan su kamar tsaftace kan hanya da sauransu.

A wani labarin kuma Jami'an Tsaro 5 Sun Mutu Yayin da Yan Bindiga da Dama Suka Sheƙa Lahira a Wani Artabu a Jihar Zamfara

Wani artabu tsakanin jami'an tsaro da yan bindiga ya laƙume rayukan yan sanda 4, da jami'in hukumar NCDC ɗaya, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Kakakin hukumar yan sandan jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel