Shugabannin Tsaro CDS, COAS, CAS, da IGP Sun Dira Maiduguri Gabanin Zuwan Shugaba Buhari

Shugabannin Tsaro CDS, COAS, CAS, da IGP Sun Dira Maiduguri Gabanin Zuwan Shugaba Buhari

  • Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, zai kai ziyarar aiki Jihar Borno ranar Alhamis
  • Manyan hafsoshin sojin ƙasar nan tare da sufetan yan sanda sun dira jihar gabanin ziyarar shugaban
  • Daga cikin waɗanda suka isa Borno akwai, CDS Lucky Iraboh, COAS Farouk Yahaya, CAS Isiaka Amao da sauran su

Gabanin ziyarar aiki da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, zai kai Maiduguri, jihar Borno, Shugaban jami'an tsaro, CDS Lucky Irabor, tare da sauran shugabannin tsaro sun dira Maiduguri, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Jami'an Tsaro 5 Sun Mutu Yayin da Yan Bindiga da Dama Suka Sheƙa Lahira a Wani Artabu a Jihar Zamfara

Da yake jawabi ga manema labarai jim kaɗan bayan fitowa daga taron operation, CDS Janar Lucky Iraboh, ya ƙara tabbatar da ƙoƙarin da jami'an tsaro suke na dawo da tsaro a ƙasar nan.

Shugabannin jami'an tsaro sun dira Maiduguri
Shugabannin Tsaro CDS, COAS, CAS, da IGP Sun Dira Maiduguri Gabanin Zuwan Shugaba Buhari Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Daga cikin waɗanda suka dira tare da CDS akwai, Hafsan sojin ƙasa, Manjo Janar Farouk Yahaya, Shugaban rundunar Sojin Sama, Air Marshal Isiaka Amao, shugaban sojin ruwa, Rear Admiral Auwal Gambo, Sufetan yan sanda na ƙasa, Usman Alƙali Baba, da sauran manyan jami'an tsaron ƙasar nan.

KARANTA ANAN: Kasar Saudiyya Ta Yanke Wa Wani Matashi Hukuncin Kisa Kan Laifin da Ya Aikata Tun Yana Yaro

CDS ya sha Alwashin kawo ƙarshen Boko Haram

Shugabannin tsaron, karaƙashin jagorancin CDS sun ziyarci sansanin rundunar Operation haɗin kai dake Maimalari.

Da yake jawabi yayin ziyarar, Janar Iraboh yace:

"Babban ƙalubalen dake gaban rundunar sojojin ƙasar nan da sauran hukumomin tsaro shine, taya za'a dawo da zaman lafiya a yankin arewa maso gabashin ƙasar nan.

"Akwai buƙatar jami'an tsaro gaba ɗaya su haɗa kan su domin cimma manufar kawo ƙarshen duk wata matsalar tsaro."

A wani labarin kuma Kada Ku Yarda Yan Bindiga Su Kashe ku, Gwamna Ya Gargaɗi Yan Sanda

Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ya roƙi jami'an hukumar yan sanda da su daina bari wasu bara gurbi suna kashe su, kamar yadda punch ta ruwaito.

Gwamnan ya faɗi haka ne yayin da yaje ta'aziyya ga hukumar a hedkwatar ta dake babban birnin jihar, Owerri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262