Alaka da Ta’addanci: Jerin Sarakuna 7 da Aka Tsige Bisa Hada Kai Da ’Yan Bindiga

Alaka da Ta’addanci: Jerin Sarakuna 7 da Aka Tsige Bisa Hada Kai Da ’Yan Bindiga

  • Jihohin Katsina da Zamfara suna ci gaba da fuskantar barazanar kashe-kashe da sace-sacen 'yan bindiga
  • Gwamnatoci sun dauki matakai don ganin an dakile munanan ayyukan 'yan ta'adda a yankunan Katsina da Zamfara
  • Daga cikin matakan, akwai dakatar da sarakunan gargajiya, wannan yasa muka tattaro jerin sarakunan da aka dakatar zuwa yanzu

Hare-haren 'yan bindiga na kara ta'azzara a yanzkin Arewa maso Gabashin Najeriya, musamman jihar Zamfara, lamarin da ya kai asarar rayuka da dama da kuma dukiyoyin da suka zarce kimantawa.

Ana zargin wasu sarakunan gargajiya da hade kai da 'yan bindiga a yankunansu, wanda yana daya daga cikin matsalolin da suka kara yawaitar aikata muggan laifuka a wasu jihohin.

A makon da ya gabata ne gwamnatin jihar Zamfara ta sake dakatar daya daga cikin manyan sarakunan jihar kan zargin alaka da 'yan bindiga, BBC ta ruwaito.

Basaraken shi ne ne na uku cikin manyan sarakuna da gwamnatin Zamfara ta dakatar, akwai kuma wasu hakimai da da gwamnati ta dakatar

Legit.ng Hausa ta tattaro rahotannin sarakuna da masu mukaman gargajiya da gwamnatin jihar ta dakatar.

KU KARANTA: Me Ya Rage Nake Nema: Masari Ya Ce Daga 2023 Zai Yi Sallama da Siyasa

1. Sarkin Zurmi

Ta'addanci: Jerin sarakuna 7 da aka dakatar saboda hada kai da 'yan bindiga
Sarkin Zurmi, Atiku Abubakar | Hoto: bbc.com/hausa
Asali: UGC

Sarkin Zurmi, Atiku Abubakar shi ne basarake na baya bayan nan da gwamnatin jihar Zamfara ta dakatar kan zargin alaka da kashe-kashen da 'yan bindiga ke yi a yankin masarautarsa, PM News ta ruwaito.

Gwamnati ta tsige shi, sannan ta umarci Bunun Kanwa, Bello Suleiman, da ya karbi jagorancin masarautar nan take.

2. Sarkin Dansadau

Ta'addanci: Jerin sarakuna 7 da aka dakatar saboda hada kai da 'yan bindiga
Sarkin Dansadau, Hussaini Umar | Hoto: bbc.com/hausa
Asali: UGC

A ranar 1 ga watan Yuni gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya dakatar da Sarkin Dansadau, Hussaini Umar kan zargin alaka da 'yan bindiga, in ji rahoton Nigerian Tribune.

Dagacin Dansadau Nasiru Muhammad Sarkin Kudu ya karɓi ragamar masarautar bayan dakatar da sarkin, kuma an kafa kwamitin bincike akansa.

3. Sarkin Maru

Ta'addanci: Jerin sarakuna 7 da aka dakatar saboda hada kai da 'yan bindiga
Sarkin Maru Abubakar Chika | Hoto: bbc.com/hausa
Asali: UGC

Rahoton Sun News ya ce, a watan Agustan 2019 gwamna Matawalle na Zamfara ya tsige Sarkin Maru Abubakar Chika bisa zargin cin amanar talakawansa ta hanyar kulla alaka da 'yan bindiga masu kashewa da satar mutane da dukiyoyi

Sai dai a nashi bangaren sarkin na Maru ya musanta zarge-zargen da ake yi wa masa.

4. Dagacin garin Kanoma

Dagacin garin Kanoma a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara, Alhaji Lawal Ahmad shi ma an dakatar da shi bisa zargin kulla alaka da masu sata da garkuwa da jama'a.

Gwamnatin Zamfara ta dakatar da shi ne tare da Sarkin Maru Abubakar Chika a shekarar 2019 bayan gano yadda 'yan bindiga ke amfani dasu wajen cutar da jama'a.

5. Dagacin Nasarawa Mailayi

An dakatar da Dagacin Nasarawa Mailayi, Bello Kiyawa, tare da sarkin Zurmi saboda zarginsu da kulla alaka da 'yan bindiga a cutar da jama'arsu.

Gwamnati ta zargi hakimin da ya hada baki da 'yan bindiga masu addabar jihar, lamarin da ya kai ga tsige shi tare da mayu gurbinsa da wani.

6. Sarkin Yakin Kanwa da Marafan Bakura

A watan Janairun 2020 gwamnatin ta dakatar da Alhaji Bello Garba Kanwa, Sarkin Yakin Kanwa da kuma da kuma Alhaji Muhammad Bello Yusuf wanda shi ne Marafan Bakura, rahoton Daily Trust ya kawo.

Gwamnatin Zamfara ta ce ta dakatar da sarakunan biyu ne bisa laifin raina gwamnati da kuma karan tsaye ga shirye-shiryenta, cin amanar al'umma da almundahana.

7. Sarkin Fawwa, Hakimin Kankara

Ta'addanci: Jerin sarakuna 7 da aka dakatar saboda hada kai da 'yan bindiga
Sarkin Fawwa, Hakimin Kankara, Alhaji Yusuf Lawal | Hoto: bbc.com/hausa
Asali: UGC

A watan Mayun 2021 aka dakatar da Sarkin Fawwa, Hakimin Kankara, Alhaji Yusuf Lawal, bisa zarginsa da ake yi masa na kulla alaka da 'yan bindiga da suka addabi jihar Katsina, in ji Daily Trust.

Masarautar Katsina ta ce ta dauki wannan mataki ne domin jaddada wa gwamnati da al'umma cewa tana goyon bayan yaki da ta'addanci da mahukunta ke yi.

Tuni aka kafa kwamitin bincike kan lamarin.

KU KARANTA: Manya Na Ku Daban: Mutumin da Ya Fi Kowa Iyalai a Duniya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

A wani labarin, Sheikh Ahmad Gumi, wani malamin addinin Islama, kuma tsohon hafsan soji, a ranar Talata, ya bayyana cewa 'yan bindiga sun gaji kuma suna son a wanzar da zaman lafiya, PM News ta ruwaito.

Shehun malamin addinin musuluncin wanda ke zaune a Kaduna yayin tattaunawa da manema labarai ya ce 'yan bindigar a shirye suke su ajiye makamansu idan suka samu hadin kai na gaske daga gwamnati.

A cikin kalaman nasa: “Eh, gaskiya ne sosai saboda 'yan bindiga suna cewa yanayi ne ya ingiza su zuwa zama 'yan bindiga.

“Idan suna da aboki na kwarai, a shirye suke su aje makamansu; sun gaji kuma suna son zaman lafiya.

“Dangane da ayyukansu, za ku fahimci cewa ko da sojoji suna fada kuma an ayyana tsagaita wuta, yakan dauki lokaci mai tsawo kafin su daina yakin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel