Me Ya Rage Nake Nema: Masari Ya Ce Daga 2023 Zai Yi Sallama da Siyasa
- Gwamnan jihar Katsina ya bayyana cewa, zai yi ritaya daga siyasa daga shekarar 2023 mai zuwa
- Gwamnan ya bayyana cewa, burinsa ya cika na yi wa 'yan jiharsa hidima, don haka zai yi ritaya zuwa gona
- Hakazalika ya bayyana alfaharinsa da jihar Katsina da ta samu shugabannin kasa har mutum biyu a tarihi
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari, ya ce zai yi ritaya daga siyasa bayan kammala wa'adinsa na Gwamna.
Masari ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da manema labarai a wani bangare na shagalin bikin ranar dimokradiyya ta kasa a Katsina ranar Asabar.
Ya bayyana cewa zai yi ritaya zuwa gonarsa bayan ya kammala wa'adinsa na Gwamnan jihar, Daily Nigerian ta ruwaito.
KU KARANTA: Yadda 'yan sanda suka kame masu hada wa 'yan ta'addan IPOB guruye da layu
“Na rike mukamai daban-daban tun daga Kwamishina a Jihar Katsina, har zuwa Majalisar Dokoki ta Kasa inda na yi aiki a matsayin Shugaban Majalisar Wakilai.
Ya kuma bayyana cewa, ya yi wa jihar Katsina hidima da aiki tukuru kuma yana ci gaba da aiki, don haka babu wani abu da yake bukata anan gaba, PM News ta ruwaito.
Ya kuma tuna, tare da bayyanawa cikin alfahari cewa, jihar Katsina ta yi shugabannin kasa har mutum biyu a Najeriya.
“Mutanena daga Katsina, kamar Marigayi Umaru Musa Yar’adua, ya tsaya takarar Shugaban kasa kuma ya ci, Muhammadu Buhari shi ma haka, kuma ya yi Shugaban kasa na mulkin soja.
"Ina ganin zai fi kyau mu bar fagen ga sauran mutane daga wasu wurare," in ji shi.
A cewarsa, babban abin da yake damunsa a yanzu shi ne yadda zai cika burinsa na dawo da martabar jihar, wanda shi ne na gyara duk wasu abubuwa da suka lalace tare da dawo da martabar abubuwan jihar da suka gabata.
Gwamnan ya ce "Bayan na yi nasarar yin hakan, zan yi ritaya zuwa gonata," in ji gwamnan.
KU KARANTA: Ba alluran Korona ke damuna na, sanya takunkumin fuska ke damuna, Shugaba Buhari
A wani labarin, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa idan ya sauka daga karagar mulki, gonarsa zai koma domin kula da shanunsa.
“Ban taba barin gonata ba. Har yanzu ina da shanu masu yawa. Zan ci gaba da zuwa gona kullum domin samun abin da zai debe mini kewa,” kamar yadda ya fada a wata hira da gidan telebijin na Arise.
Kafar telebijin din ta watsa hirar ce a ranar Alhamis da safe.
Asali: Legit.ng