Zagon Kasa: An Kori Shugaban Jam’iyyar APC Na Jihar Filato an Nada Mataimakinsa

Zagon Kasa: An Kori Shugaban Jam’iyyar APC Na Jihar Filato an Nada Mataimakinsa

  • Gwamnan jihar Filato ya tabbatar da dakatar da shugaban jam'iyyar APC na jihar bayan makwanni
  • An dakatar da shugaban ne bisa zargin yiwa jam'iyyar APC zagon kasa, lamarin da bai yi wa jam'iyyar dadi ba
  • Tuni gwamnan jihar ya sanar da nadin sabon shugaban jam'iyyar jiya Asabar a yayin taron ranar dimokradiyya

Gwamna Simon Lalong na jihar Filato ya tabbatar da tsige Cif Letep Dabang a matsayin shugaban jam'iyyar APC na jihar, Punch ta ruwaito.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a daren Asabar yayin wata liyafar cin abincin dare da aka shirya ta masu ruwa da tsaki a matsayin wani bangare na ayyukan bikin ranar Dimokiradiyya ta 12 ga Yuni wanda aka gudanar a gidan Gwamnatin Rayfield da ke Jos.

KU KARANTA: Manjo Hamza Al-Mustapha Ya Ba Shugaban Hafsan Soji Shawari Kan Yaki da Boko Haram

Gwamnan jihar Filato ya tabbatar da korar shugaban APC na jihar
Gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong | Hoto: bbc.co.uk
Asali: UGC

Lalong a jawabinsa ya gabatar da sabon Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar in da yake cewa:

“Muna da sabon shugaban jam'iyyar APC a Filato. Yana nan tare da mu. Na gan shi yana kokarin aika sakon tes ta hanyar amfani da wayarsa na ce, bari na tsaya a nan na gabatar dashi kafin ya bace mani.”

Duk da cewa Gwamnan bai kara magana a kan lamarin ba, amma an tattaro cewa ana zargin tsohon shugaban wanda Mataimakinsa, Enough Fanmak ya maye gurbinsa, da aikata zagon kasa ga jam'iyyar lamarin da ya sa aka dakatar da shi.

Dakatar da Dabang na kunshe ne a cikin wata wasika da Sakataren Jam’iyyar na Kasa, Sanata John Akpanudoedehe ya rubuta masa.

Wasikar mai dauke da kwanan wata 11 ga Yuni, 2021, ta ce,:

“Jam’iyyar na takardar da ta dakatar da kai daga ofis a matsayin Shugaban riko na Jiha na reshen Filato na jam’iyyarmu, kan yiwa jam’iyya zagon kasa."

Gwamnan ya yi tir da amfani da kafafen sada zumunta wajen yin barazana ga Najeriya

Har ila yau, an ruwaito cewa, Gwamna Simon Lalong ya yi tir da yadda ake amfani da kafofin sada zumunta wajen yin barazana ga dimokradiyyar Najeriya.

Ya ce wasu ‘yan Najeriya suna amfani da kafafen sada zumunta wajen yada manufofinsu na kashin kansu ba tare da lura ga kiyaye mutuncin dimokiradiyyar Najeriya ba.

Lalong ya ce "Wani lokacin, idan ka bi abin da wasu mutane suka sanya a kafofin sada zumunta, za ka yi tunanin anya ko sun yi imani da Najeriya?"

KU KARANTA: Duk da Kokarina, Ta’addanci Ya Dawo Zamfara Kamar Da, Gwamna Matawalle

A wani labarin, Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari, ya ce zai yi ritaya daga siyasa bayan kammala wa'adinsa na Gwamna.

Masari ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da manema labarai a wani bangare na shagalin bikin ranar dimokradiyya ta kasa a Katsina ranar Asabar.

Ya bayyana cewa zai yi ritaya zuwa gonarsa bayan ya kammala wa'adinsa na Gwamnan jihar, Daily Nigerian ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.