Iyalan MKO Abiola Sun Koka Ga Shugaba Buhari, Sun Ce Har Yanzun Basu Amfama da Komai Ba

Iyalan MKO Abiola Sun Koka Ga Shugaba Buhari, Sun Ce Har Yanzun Basu Amfama da Komai Ba

  • Iyalan Marigayi MKO Abiola sun nuna damuwarsu kan yadda gwamnatin tarayya tayi watsi da su
  • A cewar iyalan marigayin wanda ya lashe zaɓen June 12, har yanzun gwamnati ta kasa cika alƙawurran da ta yi musu
  • Kakakin iyalan, Rahaman Abiola, ya yaba wa shugaba Buhari bisa tabbatar da nasarar da kakansa ya samu a wancan Lokacin

Mambobin iyalan marigayi MKO Abiola, sun nuna rashin jin daɗin su kan yadda gwamnati tayi watsi da al'amuransu.

Mai magana da yawun gidan, Rahaman Abiola, shine ya bayyana haka ranar Asabar 12 ga watan Yuni, a jihar Ogun, yace gwamnati ta kasa cika musu alƙawarin da tayi musu a shekarun baya, kamar yadda Punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Maganar Sulhu Ta Ƙare, Zamu Ɗauki Matakin da Yan Bindiga Suka Fi Gane Wa, Matawalle

Da yake magana a Abekuta, babban Birnin jihar Ogun, Abiola yace har yanzun iyalan gidan su basu amfana da komai ba daga gwamnatin tarayya.

Iyalan MKO Abiola Sun Koka ga gwamnatin tarayya
Ka Bamu Kunya Da Ka Kasa Cika Mana Alƙawarin da Kayi mana, Iyalan MKO Abiola Ga Buhari Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Sai dai duk da haka, wakilin iyalan marigayi Abiola, ya yaba wa shugaban Ƙasa Buhari bisa girmama tsohon ɗan siyasan da muƙamin zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Najeriya, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Yace: "Munji daɗin matakin shugaba Buhari na giramama Abiola da GCFR kuma ya maida 12 ga Watan Yuni a matsayin ranar demokaraɗiyya a hukumance."

"Jinjina ga Shugaba Buhari, amma har yanzun bamu amfana da komai ba daga FG."

Hakanan kuma Rahaman Abiola ya yaba wa gwamnatin jihar Ogun kan yadda take murnar zagayowar wannan rana tare da iyalan gidan su.

KARANTA ANAN: Tsohon Ɗan Takarar Gwamna Tare da Jiga-Jigan Kwankwasiyya 27 Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC

Yace: "A duk ranar 12 ga watan Yuni, gwamnatin jihar Ogun na iyakar bakin ƙoƙarin ta, mun jinjina musu akan haka."

"Gwamna ya na zuwa har gida ya ƙara mana ƙarfin guiwa, kuma ya tabbatar da mun yi murnar wannan rana a kowace shekara."

A wani labarin kuma Gwamna Ya Bayyana Wasu Yan Siyasa Dake Samar da Motoci ga Yan Bindigan Jiharsa

Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ya zargi wasu yan siyasa da taimaka wa wajen rura wutar kai hari a jiharsa.

Gwamnan yayi wannan jawabi ne yayin da yake jawabin ranar demokaraɗiyya a gidan radio.

Asali: Legit.ng

Online view pixel