Maganar Sulhu Ta Ƙare, Zamu Ɗauki Matakin da Yan Bindiga Suka Fi Gane Wa, Matawalle

Maganar Sulhu Ta Ƙare, Zamu Ɗauki Matakin da Yan Bindiga Suka Fi Gane Wa, Matawalle

  • Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, yace zai ɗauki matakin da ya dace a kan yan bindigan da suka addabi mutane
  • Gwamnan ya bayyana cewa da farko ya ɗauki matakin sulhu kuma an samu nasara, amma yanzun za'a musu abinda suke so
  • Matawalle ya faɗi haka ne a wani jawabi da yayi wa al'ummar jihar bayan wasu munanan hare-hare da aka kai kwanan nan

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, yace gwamnatinsa zata ɗau tsattsauran mataki kan yan bindigan da suka addabi jihar da masu ɗaukar nauyin su, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Gwamna Ya Bayyana Wasu Yan Siyasa Dake Samar da Motoci ga Yan Bindigan Jiharsa

Gwamnan ya faɗi haka a wani jawabi da yayi ga al'ummar jihar a Gusau ranar Asabar, bayan yan bindiga sun kai sabbin hare-hare a jihar.

Gwamna Bello Matawalle na Jihar Zamfara
Maganar Sulhu Ta Ƙare, Zamu Ɗauki Matakin da Yan Bindiga Suka Fi Gane Wa, Matawalle Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Legit.ng hausa ta ruwaito cewa wasu ɗaruruwan yan bindiga akan mashin sun kai hari ƙauyen Kadawa, ƙaramar hukumar Zaurmi, inda suka kashe mutane da dama.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 60 a Jihar Zamfara

Gwamnan ya sake jaddada ƙudirinsa na ɗaukar mataki kan duk wani mai hannu a hare-haren da ake kaiwa jihar a baya da kuma yanzu.

Yace: "A yan makwannin nan, aikin ta'addanci ya ɗauki wani sabon salo ba kamar farkon zuwan mu kan mulki ba."

"Waɗannan mutanen suna kashe kowa ba tare da tausayi ba; mata, tsofaffi da ƙananan yara, babu wanda ya tsira a wurin su."

"Ku shaida ne kan irin namijin kokarin da gwamnatin mu tayi tun farkon zuwanta madafun iko, musamman tattaunawar sulhu da tazo da shi kuma ta samu nasara."

Matawalle ya ƙara da cewa a halin yanzu wasu bara gurbi sun sake zuwa zasu canza abinda muka gina yayin da matsalar tsaro sai ƙaruwa take a kullum.

"Addu'ata a kullum itace Allah ya tona asirin duk mai hannu akan waɗannan hare-haren. Ina mai tabbatar muku gwamnatin mu zata cigaba da ƙoƙarin da take da kawar da ayyukan ta'addanci a faɗin jihar mu."

A wani labarin kuma Tsohon Ɗan Takarar Gwamna Tare da Jiga- Jigan Kwankwasiyya 27 Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC

Tsohon ɗan takarar gwamnan Kano tare da wasu jiga-jigan PDP sun sauya sheƙa zuwa Jam'iyyar APC.

Gwamnan Jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, yace sun ɗauki matakin da ya dace kuma a lokacin da ya dace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel