Tsohon Ɗan Takarar Gwamna Tare da Jiga-Jigan Kwankwasiyya 27 Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC a Jihar Kano

Tsohon Ɗan Takarar Gwamna Tare da Jiga-Jigan Kwankwasiyya 27 Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC a Jihar Kano

  • Tsohon ɗan takarar gwamnan Kano tare da wasu jiga-jigan PDP sun sauya sheƙa zuwa Jam'iyyar APC
  • Gwamnan Jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, yace sun ɗauki matakin da ya dace kuma a lokacin da ya dace
  • Rahoto ya nuna cewa rikice ya so ya ɓarke a wurin babban taron APC a Kano, amma daga baya an saita komai

Tsoohon ɗan takarar gwamna a jihar Kano tare da wasu ɗaruruwan yan siyasa sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC a jihar, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Daga cikin waɗanda aka amshi tubarsu a wurin babban taron da APC ta gudanar a Kano akwai, Sagir Salihu Takai, tsohon ɗan takarar gwamna ƙarƙashin PDP, PRP, da ANPP, tare da Abdulsalam A. Zaura, wanda ya taɓa tsayawa takarar gwamna a jam'iyyar GNP.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Sojoji Sun Cafke Wani Riƙakken Ɗan Leƙen Asirin ISWAP a Borno

Sauran sun haɗa da, Abba Risqua Murtala Mohammed, wanda yake ɗa ne ga tsohon shugaban ƙasa a mulkin soja, Murtala Muhammad, da kuma dan majalisar tarayya mai wakiltar Ƙiru da Bebeji a majalisar wakilai, Aliyu Datti Ahmed.

Taron jam'iyyar APC a jihar Kano
Tsohon Ɗan Takarar Gwamna Tare da Jiga-Jigan Kwankwasiyya 27 Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC a Jihar Kano Hoto: dailytrust.com
Asali: Facebook

Haka zalika, daga cikin waɗanda aka ambaci sunansu da suka sauya sheƙa zuwa APC akwai wasu jiga-jigan tafiyar kwankwasiyya.

Hajiya Binta Spikin, tsohuwar mai taimakawa kan yaɗa labarai ga shugaban kwankwasiyya kuma tsohon gwamnan Ƙano, Rabi'u Musa Kwankwaso, tana daga cikin waɗanda suka koma APC.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 60 a Jihar Zamfara

Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, shine ya amshi tubarsu tare da miƙa su ga shugaban APC na riƙo, wanda Alhji Farouk Adamu Aliyu ya wakilta.

Gwamnan Kano ya bayyana cewa waɗanda suka sauya sheƙar sun ɗauki matakin da ya dace kuma a lokacin da ya dace.

Legit.ng hausa ta gano cewa rikici ya ɓarke a wajen taron yayin da Kakakin majalisar dokokin jihar Rt. Hon Hamisu Chidari, yake nasa jawabin.

Lamarin ya so tarwatsa taron yayin da mutane suka fara barin wurin, amma daga baya komai ya dawo daidai.

A wani labarin kuma Ku Gyara Halinku, Ku Tabbatar da Tsaro a Najeriya Idan Kuna Son Aikin Yi, Buhari ga Matasa

Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari , ga gargaɗi matasan Najeriya da su gyara halin su idan suna son aikin yi, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Buhari ya faɗi hakane yayin wata fira da yayi da kafar watsa labarai ranar Alhamis da safe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262