Gwamna Ya Bayyana Wasu Yan Siyasa Dake Samar da Motoci ga Yan Bindigan Jiharsa

Gwamna Ya Bayyana Wasu Yan Siyasa Dake Samar da Motoci ga Yan Bindigan Jiharsa

  • Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ya zargi wasu yan siyasa da taimaka wa wajen rura wutar kai hari a jiharsa
  • Gwamnan yayi wannan jawabi ne yayin da yake jawabin ranar demokaraɗiyya a gidan radio
  • Yace gwamnatinsa ta haɗa sunayen duk masu hannu akan lamarin, kuma zata bayyana wa jama'a bada jimawa ba

Gwamna Hope Uzodimma na jihar Imo, yace motocin da yan bindigan suka fi amfani da su wajen kai hare-hare a jihar, wasu yan siyasa ne suka basu a lokacin zaɓen da ya gabata, kamar yadda dailynigerian ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Tsohon Ɗan Takarar Gwamna Tare da Jiga-Jigan Kwankwasiyya 27 Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC

Da yake fira da gidan radio a ranar demokaraɗiyya, gwamnan yace gwamnatinsa ta fara tattara sunayen waɗan nan yan siyasan kuma bada jimawa zata bayyana wa jama'a, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Gwamna Hope Uzodimma na jihar Imo
Gwamna Ya Bayyana Wasu Yan Siyasa Dake Samar da Motoci ga Yan Bindigan Jiharsa Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

A cewar gwamnan, da irin waɗannan motocin aka kai hari gidan gyaran hali dake Owerri ranar 5 ga watan Afrilu, Hedkwatar jami'an gyaran hali (NCoS), inda fursunoni da yawa suka tsere.

Mr. Uzodimma ya ƙara da cewa daga baya an samu nasarar kamo wasu daga cikin fursunonin da suka tsere.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Sojoji Sun Cafke Wani Riƙakken Ɗan Leƙen Asirin ISWAP a Borno

Yace: "Mafi yawancin motocin Sienna da yan bindigan suka yi amfani da su yayin kai harin, yan siyasa ne suka samar musu lokacin yaƙin neman zaɓe, kuma suka gaza ƙwace su bayan kammala zaɓe."

"Mun haɗa sunayen waɗannan yan siyasan kuma bada jimawa ba zamu bayyana wa mutane kowa yasan su."

"Babu wata gwamnati da zata zauna tana kallo yan ta'adda su mamaye jihar ta."

A wani labarin kuma Wasu Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum Aƙalla 60 a Jihar Zamfara

Wani shaida ya bayyana cewa maharan sun shiga ƙauyen ne da misalin ƙarfe 6:00 na yammacin ranar Alhamis, inda suka kashe mutum 54.

A cewarsa, yan bindigan sun yi awon da gaba da shanu da dama, sannan sun shiga shaguna sun ɗebi kayayyaki da yawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262