Buhari bai hana Twitter ba, APC ta bayyana manufar shugaban kasa

Buhari bai hana Twitter ba, APC ta bayyana manufar shugaban kasa

- Jam'iyyar APC ta bayyana cewa, shugaba Buhari bai hana yin Twitter ba kwata-kwata a kasar

- Jam'iyyar ta bayyana yadda lamarin yake da cewa, shugaban ya dakatar da Twitter ne ba hani ba

- Jam'iyyar ta kuma shaida cewa, ana kan tattaunawa da gwamnati don ganin an daidaita tsakani

Shugaban Matasan na kasa na jam’iyyar APC, Ismaeel Ahmed, a ranar Laraba, ya ce Gwamnatin Tarayya ba ta hana amfani da Twitter ba, kawai ta dakatar da ayyukan ta ne.

Ya fadi haka ne a wani taron manema labarai da yake gabatarwa wanda aka sake tsarawa domin ci gaban taron matasa wanda zai gudana a mako mai zuwa, Punch ta ruwaito.

KU KARANTA: Da dumi: dumi: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da matan aure 3 a jihar Kaduna

Buhari bai hana Twitter, APC ta bayyana manufar shugaban kasa
Buhari bai hana Twitter, APC ta bayyana manufar shugaban kasa Hoto: thenationonlineng.net
Asali: Twitter

Ahmed ya ce:

“Gwamnati ba ta hana shafukan sada zumunta ba kamar yadda mutane da yawa za su yi zato.
Yana da mahimmanci mu sani cewa Facebook har yanzu yana aiki, Instagram har yanzu yana aiki, WhatsApp yana aiki, kuma da yawa sauran dandamali na dandalin sada zumunta duk suna aiki.
“A zahiri, wasu mutane za su ce maka Twitter na fitattun matasa ne kuma ba lallai ne ya zama gama gari ba.
“Ina ganin akwai masu yin Facebook da yawa a Najeriya fiye da Twitter. Amma, har yanzu kafa ce mai mahimmanci ga mutane.
“Don haka, duk abin da gwamnati ta ji na dakatar da Twitter, ba na hanawa ba, akwai dakatarwar, kuma ba shakka, akwai tattaunawa da ke gudana tsakanin gwamnati da wakilan Twitter kuma na tabbata za a warware matsalar.”

Ismaeel wanda jigo ne a APC ya kuma ce yayin da shi kansa ba ya farin ciki da dakatar da ayyukan shafin na yanar gizo, ba shi da wata matsala ta bayyana tarayyarsa da gwamnatin tarayya don daukar matakin.

'Yan Najeriya da dama na kokawa kan dakatar da kafar sadarwar Twitter da gwamnatin Buhari tayi, lamarin ya jawo cece-kuce tsakanin fitattun 'yan Najeriya wanda har gwamnati ta ce za ta hukunta duk wanda aka kama da hawa shafin na Twitter, BBC ta rahoto.

KU KARANTA: Bankuna a Najeriya sun fara jan cajin USSD N6.98, masana sun bayyana illar haka

A wani labarin, Lauyan kare hakkin dan Adam kuma Babban Lauyan Najeriya, Femi Falana, ya ce Gwamnatin Buhari ta yi kuskure wajen dakatar da ayyukan Twitter a kasar.

A cewar Falana, a tsarin dimokiradiyya, ba a ba wa gwamnati damar yanke hukunci kai da kai ba, wanda hakan ke nuna cewa maimakon sanya haramcin, kamata ya yi gwamnatin ta “kai karar Twitter idan kamfanin ya ki amsawa damuwar gwamnati ”.

A cewar babban lauyan cikin wata hira da Channels Television cikin shirin Sunrise Daily, ya kamata Gwamnatin Tarayya ta kasance ko dai ta shigar da kara kan Twitter a Amurka ko kuma a Ghana inda kamfanin ke da hedikwatar Afirka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel