Ba daidai bane dakatar da Twitter: Falana ya bayyana abinda ya kamata Buhari ya yi

Ba daidai bane dakatar da Twitter: Falana ya bayyana abinda ya kamata Buhari ya yi

- Babban lauyan Najeriya Femi Falana ya bayyana abinda gwamnatin Buhari ya kamata ta yi ba dakatar da Twitter ba

- A cewarsa, ya kamata gwamnatin Buhari ta kai karar kamfanin na Twitter ne kasar Amurka ko Ghana don jin ta bakinta

- Ya kuma bayyana cewa, hana Twitter din tauye hakkin 'yan kasa ne na samun bayanai da fadin albarkacin baki

Lauyan kare hakkin dan Adam kuma Babban Lauyan Najeriya, Femi Falana, ya ce Gwamnatin Buhari ta yi kuskure wajen dakatar da ayyukan Twitter a kasar.

A cewar Falana, a tsarin dimokiradiyya, ba a ba wa gwamnati damar yanke hukunci kai da kai ba, wanda hakan ke nuna cewa maimakon sanya haramcin, kamata ya yi gwamnatin ta “kai karar Twitter idan kamfanin ya ki amsawa damuwar gwamnati ”.

A cewar babban lauyan cikin wata hira da Channels Television cikin shirin Sunrise Daily, ya kamata Gwamnatin Tarayya ta kasance ko dai ta shigar da kara kan Twitter a Amurka ko kuma a Ghana inda kamfanin ke da hedikwatar Afirka.

KU KARANTA: Rohoto: Tattalin arzikin Najeriya ya karu, zai habaka a shekaru 3, Bankin Duniya

Ba daidai ne dakatar da Twitter: Falana ya bayyana abinda ya kamata Buhari ya yi
Ba daidai ne dakatar da Twitter: Falana ya bayyana abinda ya kamata Buhari ya yi Hoto: stackpathcdn.com
Asali: UGC

A nasa ra'ayin, Falana ya ce babu wani tushe da za a iya tabbatar da abin da gwamnati ke zargi. Ya kara da cewa ba za a hana masu amfani da Twitter miliyan 40 amfani da kafar ba saboda son kai na mutum daya.

'Yan Najeriya sun nuna fushinsu bayan da gwamnatin tarayya a ranar Juma'a da ta gabata ta sanar da dakatar da amfani da shafin Twitter, kafar yada labarai da 'yan kasar ke amfani da ita na tsawon shekaru don bayyana ra'ayoyinsu.

Femi Falana, ya fada wa Premium Times cewa dakatarwar ta kasance "tauye hakki" ga 'yancin 'yan Najeriya na fadin albarkacin baki ciki har da 'yancin samun bayanai a kasar.

KU KARANTA: Makinde: A bamu dama mu damka wa 'yan bangan Amotekun bindiga AK-47

A wani labarin daban, Jam’iyyar APC ta fadakar da ‘yan Najeriya game da hadurran da ke tattare da samun bayanai, musamman a kafofin sada zumunta ta amfani da Virtual Private Network (VPN).

Sanarwar ta ce yana da matukar sauki ga munanan ayyukan masu satar bayanai wadanda za su iya satar bayanai da kudade a asusun banki su sauka kan 'yan Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Sakataren kwamitin kula na rikon kwarya na jam'iyyar APC, Sanata John James Akpanudoedehe ne ya bayyana haka a ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel