Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin El-Rufa'i Tayi Magana Kan Cafke Yan Bindigan da Suka Sace Ɗaliban Greeenfield

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin El-Rufa'i Tayi Magana Kan Cafke Yan Bindigan da Suka Sace Ɗaliban Greeenfield

- Gwamnatin jihar Kaduna ta yi bayani game da rahoton dake yawo cewa an kama yan bindigan da suka sace ɗaliban Greenfield

- Kwamishinan tsaro na jihar, Samuel Aruwan, yace gwamnati bata labarin kama yan ta'addan

- Mr. Aruwan yace hukumomin tsaro b su turo musu bayani game da sahihancin rahoton ba

Gwamnatin jihar Kaduna ta musanta rahoton da ake yaɗawa cewa an samu nasarar cafke yan bindigan da suka sace ɗalibai a jami'ar Grienfield dake jihar Kaduna.

KARANTA ANAN: Mun Shiga Ƙuncin Rayuwa Saboda Tsare Mahaifanmu, 'Ya'yan El-Zakzaky Sun Koka

Kwamishinan tsaro da al'amuran cikin gida, Samul Aruwan, shine yayi martani kan rahoton kama yan bindigan.

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin El-Rufa'i Tayi Mgana Kan Cafke Yan Bindigan da Suka Sace Ɗaliban Greeenfield
Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin El-Rufa'i Tayi Mgana Kan Cafke Yan Bindigan da Suka Sace Ɗaliban Greeenfield Hoto: Samuel Aruwan FB Fage
Asali: Facebook

Mr Aruwan yayi maratanin ne a wani gajeren rubutu da yayi a shafinsa na dandalin sada zumunta Facebook ranar Laraba.

KARANTA ANAN: An Kuma, Yan Bindiga Sun Sake Yin Awon Gaba da Malamin Jami'ar UNIJOS

Yayin da yake martani kan rahoton, Kwamishina Aruwan Yace:

"Ina ta samun kiraye-kirayen waya, saƙonnin waya, da saƙon email, ana tambaya ta in tambatar da gaskiyar labarin da ake yaɗawa cewa an kama yan bindigan da suka sace ɗaliban jami'ar Greenfield."

"Duk da cewa muna buƙatar muga an kama su, amma a halin yanzun ba zan iya tabbatar da sahihancin rahoton dake yawo ba, kuma ni har yanzun ban samu wani bayani daga hukumomin tsaro kan lamarin ba."

Legit.ng hausa ta gano rahoton wanda ya nuna cewa jami'an tsaro sun kama wasu dauke da mukudan kuɗaɗe da ake zargin kuɗin fansa ne tare da makamai a tare da su, waɗanda ake zargin cewa sune yan bindigan da suka sace ɗaliban Greenfield ne.

A wani labarin kuma Gwamnatin Tarayya Ta Fito da Wani Sabon Tsari, Zata Tallafawa Yan Najeriya Miliyan Ɗaya da N5,000 na Tsawon Wata 6

Gwamnatin tarayya zata tallafawa yan Najeriya kimanin miliyan ɗaya da kuɗi N5,000 na tsawon watanni 6.

Gwamnatin tace an kaddamar da shirin tun farkon wannan shekarar kuma wasu mutane sun amfana da shi a Lagos da Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel