An Kuma, Yan Bindiga Sun Sake Yin Awon Gaba da Malamin Jami'ar UNIJOS

An Kuma, Yan Bindiga Sun Sake Yin Awon Gaba da Malamin Jami'ar UNIJOS

- Wasu yan bindiga sun kutsa gidan malamin jami'ar UNIJOS, inda duka yi awon gaba da shi

- Rahotanni sunce maharan sun isa yankin da gidan malamin yake da misalin ƙarfe 2:00 na dare

- Shugaban ASUU, reshen UNIJOS, Dr. Lazarus Maigoro, ya tabbatar da sace malamin jami'ar

Yan bindiga sun yi awon gaba da malamin jami'a, Dr. Dan Ella, dake aiki a jami'ar Jos (UNIJOS), jihar Plateau, kamar yadda Punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Wata Ɗalibar Jami'ar BUK Ta Rigamu Gidan Gaskiya a Gidan Kwanan Ɗalibai

Yan bindigan sun sace malamin ne da safiyar ranar Laraba, a gidansa dake yankin gidaje na 'Haske quarters', garin Lamingo, ƙaramar hukumar Jos ta arewa, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Wurin da aka sace malamin shine wurin da wasu yan bindiga suka sace wata Farfesa da mijinta a watan da ya gabata, amma daga baya sun sake su bayan an basu kuɗin Fansa.

An Kuma, Yan Bindiga Sun Sake Yin Awon Gaba da Malamin Jami'ar UNIJOS
An Kuma, Yan Bindiga Sun Sake Yin Awon Gaba da Malamin Jami'ar UNIJOS Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Wani magidanci dake yankin da abun ya faru, Philip Gyang, ya tabbatar da ɗauke malamin ga jaridar Punch da safiyar ranar Laraba.

Gyang yace yan bindigan sun shigo yankin da misalin ƙarfe 2:00 na dare inda suka nufi gidan malamin kai tsaye, suka yi awon gaba da shi.

KARANTA ANAN: FG Ta Fito da Wani Sabon Tsari, Zata Tallafawa Yan Najeriya Miliyan Ɗaya da N5,000 na Tsawon Wata 6

Gyang yace: "Abinda ya faru a yankin Haske Quaters jiya da daddare ba shi da daɗi. Ƙarar bindiga ce ta tashe mu daga bacci wajen ƙarfe 2:00 na dare, kuma babu damar fita sabida yan bindiga ne suka kawo hari."

"Da safe ne muka samu damar fitowa, inda muka gano cewa sun yi awon gaba da, Dr. Dan Ella, bayan ɓalla kofar gidan shi."

Shugaban ƙungiyar malaman jami'o'i ASUU reshen UNIJOS, Dr Lazarus Maigoro, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Da aka tuntuɓi Kakakin hukumar yan sandan jihar Plateau, Ubah Ogaba, ba'a same shi bare yayi tsokaci kan lamarin ba.

A wani labarin kuma FG Ta Yi Ƙarin Haske Kan N-Power, Tace Mutum 550,000 Ne Suka Tsallake Matakin Tantancewa

Gwamnatin tarayya ta yi ƙarin haske kan matakin da ake na ɗaukar ma'aikata a shirin N-Power, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Ministan Ma'aikayar jin ƙai da walwala, Sadiya Farouq, ita ce tayi jawabi dangane da shirin yau a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262