Mun Shiga Ƙuncin Rayuwa Saboda Tsare Mahaifanmu, 'Ya'yan El-Zakzaky Sun Koka

Mun Shiga Ƙuncin Rayuwa Saboda Tsare Mahaifanmu, 'Ya'yan El-Zakzaky Sun Koka

- Iyalan Sheikh Ibrahim El-zakzaky, shugaban ƙungiyar mabiya shi'a IMN, sun bayyana irin halin da suke ciki na rashin iyayen su

- Ɗaya daga cikin yayan malamin, Suhaila Ibrahim, ita ce ta faɗi haka a wata fira da tayi da kafar watsa labarai

- Tace a halin yanzun ba su samun damar ganin iyayen su a lokacin da suke buƙata

'Yaƴan shugaban ƙungiyar shi'a (IMN), Sheikh Ibrahim El-zakzaky, sun koka kan yadda gwamnati ta tsare iyayen su fiye da kwana 2,000 a hannun jami'an tsaro.

KARANTA ANAN: An Kuma, Yan Bindiga Sun Sake Yin Awon Gaba da Malamin Jami'ar UNIJOS

A wata zantawa da ɗaya daga cikin ƴaƴan Zakzaky, Suhaila Ibrahim El-zakzaky, tayi da BBC ta bayyana cewa a halin yanzun ba su da wani buri da ya wuce suga iyayen su a tare da su.

Legit.ng hausa ya gano cewa a ranar Alhamis 3 ga watan Yuni, 2021, Zakzaky ya cika kwanaki 2,000 cif a tsare, bayan kama shi da jami'an tsaro suka yi a watan Disamba, 2015 a gidansa dake Zariya.

Mun Shiga Ƙuncin Rayuwa Saboda Tsare Mahaifanmu, 'Ya'yan El-Zakzaky Sun Koka
Mun Shiga Ƙuncin Rayuwa Saboda Tsare Mahaifanmu, 'Ya'yan El-Zakzaky Sun Koka Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Suhaila ta koka ga gwamnatin tarayya kan yadda ta cigaba da tsare mahifan su duk da kotu ta bada belin su.

Ɗiyar Zakzaky tace: "Babban burin mu a yanzun shine muga an sako mahaifanmu, tun da laifin da ake zargin shi da aikatawa, an saki sauran waɗanda ake tuhumar su da laifin."

"To don me za'a cigaba da tsare su, ko don ance su suka sa a aikata laifin?"

KARANTA ANAN: FG Ta Fito da Wani Sabon Tsari, Zata Tallafawa Yan Najeriya Miliyan Ɗaya da N5,000 na Tsawon Wata 6

Suhaila ta ƙara da cewa yanzun an kai matakin da ba'a barin su ga mahaifan nasu akai akai kamar yadda suke yi a baya.

Hakazalika ta bayyana cewa har yanzun akwai sauran raunin harbi a jikin mahaifansu, wanda aka ji musu lokacin da aka je kama su, kuma ba'a basu kulawar da ta kamata ba a inda suke tsare.

Tace: "A halin yanzun muna cikin mawuyacin hali, tashin hankali da wahala, saboda raba mu da iyayen mu na tsawon waɗannan kwanaki."

"Ba zamu gan su sanda muke so ba, ba zamu nuna musu kulawa ba, wannan babban abun tashin hankali ne."

A wani labarin kuma Wata Ɗalibar Jami'ar BUK Ta Rigamu Gidan Gaskiya a Gidan Kwanan Ɗalibai

Wata ɗaliba dake ajin ƙarshe a jami'ar BUK Kano ta rigamu gidan gaskiya bayan fama da gajeriyar rashin lafiya, kamar yadda punch ta ruwaito.

Ɗalibar mai suna, Mercy Sunday, ta mutu ne a safiyar ranar Talata kamar yadda ƙawarta ta faɗa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262