FG Ta Fito da Wani Sabon Tsari, Zata Tallafawa Yan Najeriya Miliyan Ɗaya da N5,000 na Tsawon Wata 6
- Gwamnatin tarayya zata tallafawa yan Najeriya kimanin miliyan ɗaya da kuɗi N5,000 na tsawon watanni 6
- Gwamnatin tace an kaddamar da shirin tun farkon wannan shekarar kuma wasu mutane sun amfana da shi a Lagos da Abuja
- Ministan ma'aikatar jin ƙai da walwala, Sadiya Farouk, ita ce ta bayyana haka ranar Talata a Abuja
Gwamnatin tarayya ta bayyana a ranar Talata cewa, yan Najeriya kimanin mutum miliyan ɗaya da cutar COVID19 ta shafa zasu samu tallafin Naira N5,000 duk wata na tsawon watanni shida, kamar yadda the nation ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: FG Ta Yi Ƙarin Haske Kan N-Power, Tace Mutum 550,000 Ne Suka Tsallake Matakin Tantancewa
Gwamnatin tace an riga amfara shirin tun farkon wannan shekarar, inda mutum 3,115 suka amfana daga jihohin Lagos da Abuja.
Tace za'a faɗaɗa shirin zuwa dukkan jihohin ƙasar nan, kuma waɗanda suka cancanta zasu fara samun tallafin ba da jimawa ba.
Ministan ma'aikatar jin ƙai da walwala, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ita ce ta bayyana haka a Abuja yayin da take jawabi a kan shirye-shiryen gwamnatin tarayya na tallafawa yan ƙasa (NSIP).
KARANTA ANAN: Bayan Sa Labule da Buhari, Gwamna Ya Bayyana Shirin Wasu Gwamnonin Ƙasar Nan Kafin Zaɓen 2023
Ministan tace wannan shiri ne na musamman da zai tallafa wa yan Najeriya masu aikin yau da kullum waɗanda annobar cutar korona ta shafa.
Ta ƙara da cewa a halin yanzu an kusa kammala tsarin waɗanda zasu amfana a rukuni na biyu, kuma da zaran an gama za'a bayyana wa yan Najeriya.
Tace: "Ma'aikatar jin ƙai da walwala na cigaba da aiki tuƙuru wajen aiwatar da shirye-shiryen tallafawa yan ƙasa domin cika ƙudirin shugaban ƙasa na tsamo yan Najeriya 100 miliyan daga cikin talauci a shekara 10."
A wani labarin kuma Wani Kwamishina Ya Rasa Muƙaminsa Saboda Yaƙi Bin Gwamna Zuwa APC
Gwamna Ben Ayade na jihar Cross Rivers ya sake sallamar wani kwamishinansa daga muƙaminsa, kamar yadda punch ta ruwaito.
Wannan na zuwa ne mako ɗaya bayan gwamnan ya sallami wasu kwamishinoninsa hudu saboda sun ƙi bin shi zuwa APC.
Asali: Legit.ng