Rashin tsaro: A karshe kungiyar Ohanaeze ta yarda zata gana da dattawan Arewa, ta kafa ajanda

Rashin tsaro: A karshe kungiyar Ohanaeze ta yarda zata gana da dattawan Arewa, ta kafa ajanda

- Ohanaeze Ndigbo ta koka kan yawaitar kashe-kashe da lalata dukiya a yankin kudu maso gabashin kasar

- Kungiyar ta ce idan har ba’a dauki matakin da ya dace don magance matsalar ba, kasar na iya fadawa cikin wani mawuyacin hali a 'yan kwanakin da ke tafe

- Cif Emmanuel Iwuanyanwu, shugaban kungiyar dattawan Ohaneze Ndigbo, ya bayyana damuwar a ranar Talata, 8 ga Yuni

Biyo bayan yawan sace-sacen mutane da kashe-kashen da ake yi a wasu sassan kasar, musamman yankin kudu maso gabas, kungiyar koli ta zamantakewar al’umman Ibo, Ohanaeze Ndigbo, ta yanke shawarar tattaunawa da shugabannin arewa kan yadda za a kame mummunan halin da ake ciki.

Jaridar The Sun ta ruwaito kawai cewa shugaban majalisar dattawan Ohaneze Ndigbo, Cif Emmanuel Iwuanyanwu, ya bayyana cewa yana kokarin hada taron dattawan daga shiyyoyin biyu don tsara yadda za a magance matsalolin.

KU KARANTA KUMA: APC ta cancanci lashe zabe na gaba a Najeriya, in ji Uzodinma

Rashin tsaro: A karshe kungiyar Ohanaeze ta yarda zata gana da dattawan Arewa, ta kafa ajanda
Rashin tsaro: A karshe kungiyar Ohanaeze ta yarda zata gana da dattawan Arewa, ta kafa ajanda Hoto: Ohanaeze Ndigbo
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa Iwuanyanwu ya bayyana abubuwan da ke faruwa a kasar a matsayin masu matukar girgiza kuma gaba daya ya zarta yadda ake tsammani da tunanin dan adam.

Ya kuma yi kira ga babban shugaban Ohaneze Ndigbo, Farfesa George Obiozor da ya shirya taron ba tare da bata lokaci ba.

Najeriya ba za ta iya jure wani Yaƙin basasa ba

A cewarsa, mutane ba sa son sake ganin abin da ya faru a shekarar 1966, saboda haka, sun yi kira ga nutsuwa da zaman lafiya tsakanin kabilun kasar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An gabatarwa Buhari da wayar hannu na farko da aka yi a Najeriya

Iwuanyanwu ya kuma jajantawa dangin marigayi tsohon mai bai wa tsohon shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa, Goodluck Jonathan, Ahmed Gulak kan mummunan kisan da aka yi masa a Owerri.

Ya ce tun lokacin da abin ya faru, ya samu kiraye-kiraye daga ‘yan Najeriya daga kowane bangare na rayuwa a cikin kasar da ma wasu kasashen da ke nuna juyayin mutuwarsa.

Dattijon ya ce:

“A madadin kungiyar dattawa ta Ohaneze Ndigbo muna nuna juyayi ga dangin dan uwanmu kuma amininmu Dakta Ahmed Gulak, Arewa da sauran kungiyoyin arewa, Gwamnati da mutanen Jihar Adamawa ciki har da abokansa da hadimansa."

Ya kuma jajantawa duk wadanda suka rasa yan uwansu sakamakon rashin tsaro a duk fadin kasar.

Kudu ta hadewa arewa kai - Kungiyar Dattawan Arewa sun koka, sun zargi Buhari

A wani labarin, kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta zargi shugabanni a yankunan kudancin Najeriya da hadewa arewa kai.

Kungiyar ta koka kan yadda lamarin ya sanya fargaba a zukatan ‘yan Arewa, musamman Fulani da ke zaune a sassa daban-daban na kasar, jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito.

Kakakin NEF, Dakta Hakeem Baba-Ahmed, a cikin wata sanarwa a ranar Talata, 25 ga Mayu, ya yi ikirarin cewa shugabannin kudu maso gabas a yanzu suna kullawa gwamnatin tarayya tuggu da kiraye-kirayen ballewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel