APC ta cancanci lashe zabe na gaba a Najeriya, in ji Uzodinma

APC ta cancanci lashe zabe na gaba a Najeriya, in ji Uzodinma

- Gwamna Hope Uzodinma ya yi ikirarin cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta cancanci lashe babban zaben 2023

- A cewar gwamnan na jihar Imo, gwamnonin jihohi na jam’iyyar adawa da yawa za su sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki

- Uzodinma ya yi ikirarin cewa wasu mutane da gangan suke kokarin kai gwamnatin shugaba Buhari kasa

A cikin abin da zai ba 'yan Najeriya da yawa mamaki, Gwamna Hope Uzodinma, ya bayyana cewa jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ta cancanci lashe babban zabe na 2023.

Gwamnan na jihar Imo ya bayyana hakan ne bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari, a fadar shugaban kasa a ranar Talata, 8 ga watan Yuni, Premium Times ta rahoto.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An gabatarwa Buhari da wayar hannu na farko da aka yi a Najeriya

APC ta cancanci lashe zabe na gaba a Najeriya, in ji Uzodinma
APC ta cancanci lashe zabe na gaba a Najeriya, in ji Uzodinma Hoto: Hope Uzodimma
Asali: Facebook

A cewarsa, gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi rawar gani, jaridar Sun ta kara da cewa.

Da yake ci gaba, gwamnan ya bayyana cewa wasu mutane na kokarin yin zagon kasa ga gwamnatin Buhari, ta hanyar hare-hare, kashe-kashe da satar mutane a fadin kasar.

KU KARANTA KUMA: Sojojin Najeriya sun dakile harin Boko Haram a Dikwa, jihar Borno

Ya ce:

“Daga cikin matsalar wannan gwamnatin shi ne yunkurin ganganci da wasu gungun mutane ke yi don su kai shi kasa.
"Saboda babu wanda yake gaya min cewa wannan gwamnatin ba ta tabuka komai, cewa ba a biyan albashi ko kuma ba a gina hanyoyi ba ko hanyar jirgin kasa ba ta tafiya ko kuma ba a bayar da kudaden tallafi daban-daban don karfafawa matasanmu gwiwa."

Bayan Ganawa da Buhari, Gwamna Ya Bayyana Shirin Wasu Gwamnonin Ƙasar Nan Kafin Zaɓen 2023

A wani labarin, Gwamna Hope Uzodimma na jihar Imo, yayi hasashen cewa APC zata samu nasara a zaɓen 2023 duk kuwa da ƙalubalen tsaron da ake fama dashi a mulkinta, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Uzodimma yayi wannan hasashe ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a fadar shugaban ƙasa jim kaɗan bayan fitowa daga ganawar sirri da shugaba Buhari.

Gwamnan yace akwai gwamnoni da dama a ƙasar nan da zasu sauya sheka zuwa APC kafin zaɓen 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel