Yanzu Yanzu: An gabatarwa Buhari da wayar hannu na farko da aka yi a Najeriya

Yanzu Yanzu: An gabatarwa Buhari da wayar hannu na farko da aka yi a Najeriya

- Gwamnatin Shugaba Buhari a ranar Laraba, 9 ga watan Yuni, ta ga wayar hannu na farko da aka kera a cikin gida

- Otunba Niyi Adebayo ne ya yi wayar kuma ya gabatar da shi ga shugaban a taron Majalisar Zartarwa na Tarayya (FEC)

- A taron FEC, Buhari ya rantsar da kwamishinonin hukumar kidaya ta kasa (NPC)

A ranar Laraba, 9 ga watan Yuni, Otunba Niyi Adebayo ya gabatarwa Shugaban kasa Muhammadu Buhari da wayar hannu na farko da aka yi a Najeriya.

An gabatar da wayar ne a yayin taron Majalisar zartarwa ta Tarayya (FEC) wanda aka gudanar a Fadar Shugaban Kasa, Abuja.

KU KARANTA KUMA: Sojojin Najeriya sun dakile harin Boko Haram a Dikwa, jihar Borno

Yanzu Yanzu: An gabatarwa Buhari da wayar hannu na farko da aka yi a Najeriya
Yanzu Yanzu: An gabatarwa Buhari da wayar hannu na farko da aka yi a Najeriya Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Bugu da ƙari, a taron, shugaban kasar ya rantsar da kwamishinonin tarayya na Hukumar Kula da Yawan Jama'a (NPC) da Hukumar Kula da ma’aikatan Tarayya (FCSC).

Kwamishinonin da aka rantsar sune Injiniya Wakil Bukar da Mohammed Dattijo Usman.

KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro: 'Yan kasuwar Arewa suna barazanar yanke hanyar samar da abinci a kasa baki daya

Hadimin shugaban kasar a kafofin watsa labarai na zamani, Buhari Sallau ne ya bayyana hakan a cikin wani wallafa da yayi a shafinsa na Facebook.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin jama’a kan wallafar:

Umar Haruna Fada ya ce:

“Wannan abin birgewa ne, muna son irin wannan rashin nasara na rantse .... Allah ya albarkaci PMB.”

Lawal Abubakar ya yi martani:

“Aiki mai kyau ya Shugaban kasa.”

Aliyu Sulaiman Idris ya ce:

“Mun yi imanin Najeriya za ta yi nasara insha Allah.”

A wani labarin, babban Bankin Duniya ya sake nazarin bunkasar tattalin arzikin da Najeriya ta yi hasashe, wanda ya kara kimanta yawan kayan cikin gida na 2021 zuwa 1.8%.

Cibiyar Bretton Wood ta daga ci gaban tattalin arzikin Najeriya daga 1.1% zuwa 1.8% na wannan shekarar, yayin da ta bayyana cewa GDP zai kara karuwa zuwa 2.1% a shekara mai zuwa, da kuma 2.4% a shekarar 2023 ta badi.

Tattalin arzikin Afirka kuwa an sake daga shi zuwa sama har 2.8% a shekarar 2021, kuma a shekara mai zuwa, tattalin arzikin yankin ana hasashen zai kai 3.3%. An kiyasta tattalin arzikin duniya cewa zai tashi da kashi 5.6%.

Asali: Legit.ng

Online view pixel