Rohoto: Tattalin arzikin Najeriya ya karu, zai habaka a shekaru 3, Bankin Duniya

Rohoto: Tattalin arzikin Najeriya ya karu, zai habaka a shekaru 3, Bankin Duniya

- Babban bankin duniya ya bayyana cewa, tattalin arzikin Najeriya ya farfado zuwa wani mataki

- Babban bankin ya bayyana bukatar hada karfi da karfe wajen tunkarar annobar Korona

- Hakazalika ya bukaci yafe bashi ga kasashe masu kananan karfi domin ci gaba da dawo da tattalin arzikin

Babban Bankin Duniya ya sake nazarin bunkasar tattalin arzikin da Najeriya ta yi hasashe, wanda ya kara kimanta yawan kayan cikin gida na 2021 zuwa 1.8%.

Cibiyar Bretton Wood ta daga ci gaban tattalin arzikin Najeriya daga 1.1% zuwa 1.8% na wannan shekarar, yayin da ta bayyana cewa GDP zai kara karuwa zuwa 2.1% a shekara mai zuwa, da kuma 2.4% a shekarar 2023 ta badi.

Tattalin arzikin Afirka kuwa an sake daga shi zuwa sama har 2.8% a shekarar 2021, kuma a shekara mai zuwa, tattalin arzikin yankin ana hasashen zai kai 3.3%. An kiyasta tattalin arzikin duniya cewa zai tashi da kashi 5.6%.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun yi kaca-kaca da masarauta, sun kone gidaje sama da 60

Rohoto: Tattalin arzikin Najeriya ya karu, zai habaka a shekaru 3, Bankin Duniya
Rohoto: Tattalin arzikin Najeriya ya karu, zai habaka a shekaru 3, Bankin Duniya Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Sabon hasashen da aka gano a lokacin annobar Korona da abin da ya biyo bayanta, ya kai ga hauhawar farashin mai, sauye-sauye na tsarin masana'antar mai, da canjin kudade mai sauki wanda ya dogara da yanayin kasuwa.

Bankin Duniya ya sanar a cikin rahotonsa na Raunin Tattalin Arzikin Duniya na watan Yunin 2021 mai taken: “Global Recovery Strong but Uneven as Many Developing Countries Struggle with the Pandemic’s Lasting Effects.”

A cikin rahoton, David Malpass, Shugaban Bankin Duniya, ya ce:

"Duk da cewa akwai alamun maraba game da farfadowar duniya, annobar na ci gaba da haifar da talauci da rashin daidaito ga mutane a kasashe masu tasowa a duniya,"

Ya kara da cewa:

“Kokarin hada karfi da karfe a duniya yana da matukar muhimmanci wajen hanzarta rarraba allurar rigakafi da kuma yafe bashi, musamman ga kasashe masu karamin karfi.
"Yayin da matsalar kiwon lafiya ta yi sauki, masu tsara manufofi za su bukaci magance matsalar ta dindindin da kuma daukar matakai na haifar da korewa, juriya, da ci gaban hada kai tare da kiyaye zaman lafiyar tattalin arziki."

KU KARANTA: Jami'an tsaro sun lalata sansanin IPOB a Imo, sun ceto wata, sun kwato bindigogi

A wani labarin, Shugaban Jami'ar Obafemi Awolowo (OAU) dake Ile-Ife, Farfesa Eyitope Ogunbodede, ya bayyana cewa maganin Korona na makarantar zai bayyana nan ba da jimawa ba.

Ya fadi haka ne a ranar Talata yayin ganawa da manema labarai a yayin bikin cikar shekaru 60 da kafuwar jami’ar, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban ya ce masu bincike daga jami’ar suna aiki tare da gwamnatocin jihohi da na tarayya don samar da magungunan Korona.

Asali: Legit.ng

Online view pixel