Jami'an tsaro sun lalata sansanin IPOB a Imo, sun ceto wata, sun kwato bindigogi

Jami'an tsaro sun lalata sansanin IPOB a Imo, sun ceto wata, sun kwato bindigogi

- Jami'an tsaro sun dira sansanin 'yan ta'addan IPOB sun lalata sansanin a wani yankin jihar Imo

- Rahotanni sun bayyana cewa, mazauna yankin sun tsere ganin yadda lamarin yazo da hadari

- Sojojin sun ceto wata jami'ar 'yar sanda da 'yan ta'addan suka sace suka boye a sansanin nasu

Jami'an tsaro na soji, 'yan sanda da sojin sama sun lalata daya daga cikin sansanonin kungiyar tsaro ta Gabas da ke da alaka da 'yan asalin yankin Biafra, Punch ta ruwaito.

Lalacewar ta afku ne a Amii-Akabo, da ke karamar hukumar Ikeduru ta jihar, biyo bayan kashe shugaban kungiyar ‘yan bindiga a jihar, wanda aka fi sani da Dragon.

Majiyar ‘yan sanda ta shaida cewa daya daga cikin 'yan kungiyar, Osinachi Stanley, ya jagoranci sojoji zuwa sansanin inda aka ceto wata mata ’yar sanda mai mukamin sufeto da ke tsare.

KU KARANTA: Jami'ar Najeriya ta kera maganin Korona, saura kiris a sake shi

Jami'an tsaro sun mamaye sansanin IPOB a Imo, mazauna sun tsere
Jami'an tsaro sun mamaye sansanin IPOB a Imo, mazauna sun tsere Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Wani dan asalin garin ya ce jami'an tsaro sun lalata gidaje akalla 10.

Wani mazaunin garin ya ce:

“Wanda aka kama da rai ne ya jagoranci jami’an tsaro zuwa kauyenmu inda aka ceto wata sufeto ta 'yan sanda da ’yan kungiyar suka yi garkuwa da ita. Akalla gidaje 10 jami'an tsaro suka lalata a kauyen mu. A yanzu haka da nake magana da ku, danginmu na kan gudu.”

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Bala Elkana, ya shaida cewa jami'an tsaron sun kutsa cikin sansanin, sun kubutar da 'yar sandar da ake tsare da ita a sansanin tare da kwato bindigogin da 'yan ta'addan suka sace daga ofisoshin 'yan sanda da suka kai hari a jihar.

A baya rundunar Sojin Najeriya ta ce mutanenta daga runduna ta shida ta Garrison, Fatakwal da Bataliya ta 29, tare da hadin gwiwar wasu jami'an tsaro, sun kashe mambobi bakwai na kungiyar tsaro ta Gabas (ESN), kungiyar masu fafutikar kafa kasar Biafra, IPOB, Premium Times.

KU KARANTA: APC ta gargadi 'yan Najeriya kan illolin amfani da VPN wajen hawa Twitter

A wani labarin, An shiga fargaba a garin Igangan, jihar Oyo, a daren Asabar, 5 ga Yuni, yayin da wasu 'yan bindiga suka tura sama da mutane 45 zuwa kabari.

Sun News ta ruwaito cewa barnar da aka kwashe sa’o’i biyar ana yi a daya daga cikin manyan garuruwan Ibarapaland ta kai ga kone gidaje sama da 60, yayin da sama da motoci 160 kuma suka lalace.

Maharan sun yi kaca-kaca da fadar Ashigangan ta Igangan, Oba Lasisi Adeoye, da kuma wani gidan mai, yayin da suka afka wa al'ummar da misalin karfe 11 na dare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.