Jami'ar Najeriya ta kera maganin Korona, saura kiris a sake shi
- Jami'ar Obafemi Awolowo ta kera maganin Korona, ta bayyana nan kusa za ta sake shi bayan bincike
- Jami'ar ta bayyana cewa, masu bincike a jami'ar na aiki da gwamnatoci wajen samar da wannan magani
- A baya can, gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa, tana kan kera allurar rigakafin Korona a kasar
Shugaban Jami'ar Obafemi Awolowo (OAU) dake Ile-Ife, Farfesa Eyitope Ogunbodede, ya bayyana cewa maganin Korona na makarantar zai bayyana nan ba da jimawa ba.
Ya fadi haka ne a ranar Talata yayin ganawa da manema labarai a yayin bikin cikar shekaru 60 da kafuwar jami’ar, Daily Trust ta ruwaito.
Shugaban ya ce masu bincike daga jami’ar suna aiki tare da gwamnatocin jihohi da na tarayya don samar da magungunan Korona.
KU KARANTA: APC ta gargadi 'yan Najeriya kan illolin amfani da VPN wajen hawa Twitter
Ya ce OAU ta lashe kyaututtuka iri-iri na bincike ciki har da gasar duniya na COVID-19 African Rapid Grant Fund, ya kara da cewa cibiyar tana samun nasarori a bincikenta.
Ya ce; “Yin aiki tare da gwamnatocin jihohi da na tarayya, masu bincikenmu sun iya samar da wasu kayayyaki wadanda za su yi matukar amfani wajen danne alamomin cutar Korona. Muna nan daram a kan lamarin.”
A wani ci gaba da aka samu cikin watan Afrilu, Najeriya ta fara gwajin asibiti na allurar rigakafin Korona da aka kera a kasar.
Shugaban kwamitin shugaban kasa kan Korona, Boss Mustapha ya fada wa manema labarai cewa za a yi amfani da alluran ne bayan kammala gwaji da kuma samun takardar shedar da ta dace, Africa News ta ruwaito.
KU KARANTA: Da duminsa: Majalisa za ta bincika dalilin hana Twitter, ta gayyaci Lai Mohammed
A wani labarin, Hukumar gudanarwar Jami'ar Jihar Kaduna (KASU) ta bayyana cewa, ta dakatar da ayyukan karatu na daliban digiri na farko a makarantar zuwa wani lokacin da ba ta ayyana ba.
Sai dai, hukumar gudanarwar ta bayyana wasu fannonin karatun da ba ta dakatar dasu ba, kamar yadda yazo a sanarwar da ta fitar a yau Talata 8 ga watan Yunin 2021.
Cikin wata sanarwa da Legit.ng Hausa ta samu, hukumar gudanarwar ta KASU ta fidda sanarwar mai nuni da dakatar da ayyukan karatu, amma ta umarci ma'aikatan makarantar da su ci gaba da zuwa aiki kamar yadda suka saba.
Asali: Legit.ng