'Yan bindiga sun yi kaca-kaca da masarauta, sun kone gidaje sama da 60

'Yan bindiga sun yi kaca-kaca da masarauta, sun kone gidaje sama da 60

- Rahotanni sun ce an kai hari gidan wani sarkin gargajiya a garin Igangan inda aka yi kaca-kaca da gidan

- An kone gidaje sama da 60 a yankin, tare da lalata motoci sama da 160 a cikin dare daya yayin harin

- Wani daga cikin ministocin Buhari ya yi Allah wadai da wannan mummunan hari tare da yin kira ga zaman lafiya

An shiga fargaba a garin Igangan, jihar Oyo, a daren Asabar, 5 ga Yuni, yayin da wasu 'yan bindiga suka tura sama da mutane 45 zuwa kabari.

Sun News ta ruwaito cewa barnar da aka kwashe sa’o’i biyar ana yi a daya daga cikin manyan garuruwan Ibarapaland ta kai ga kone gidaje sama da 60, yayin da sama da motoci 160 kuma suka lalace.

Maharan sun yi kaca-kaca da fadar Ashigangan ta Igangan, Oba Lasisi Adeoye, da kuma wani gidan mai, yayin da suka afka wa al'ummar da misalin karfe 11 na dare.

KU KARANTA: Bidiyon dan Najeriya mazaunin Turai: Zan dawo da tankar yaki na shiga Sambisa

Yankin Yarbawa ya rikice, 'yan bindiga sun kone gidaje 60 har da na sarkin gargajiya
Yankin Yarbawa ya rikice, 'yan bindiga sun kone gidaje 60 har da na sarkin gargajiya Hoto: oyoinsight.com
Asali: Twitter

A cewar rahoton, majiyoyi sun bayyana cewa maharan wadanda yawansu ya kai 50 a kan babura sama da 20 sun yi barna har zuwa misalin karfe 4 na safiyar ranar Lahadi, 6 ga Yuni, kafin su bar garin.

Taiwo Adeagbo, sakataren kungiyar manoma a Igangan da yake magana a kan lamarin ya ce an rasa rayuka da dama yayin barnar.

Adeagbo ya kara da cewa an harbe mazauna garin da dama, yayin da wasu jami'an tsaro suka kashe wasu daga cikin maharan.

Sunday Dare, ministan matasa da ci gaban wasanni na Najeriya yayi Allah wadai da harin da aka kai a Igangan wanda ya haifar da asarar rayuka da dukiyoyi.

Dare, a cikin wata sanarwa da ofishin yada labaransa ya fitar, ya bayyana abin da ‘yan bindigan suka yi a matsayin zunzurutun mugunta, dabbanci da rashin kirki, rahoton jaridar Nigerian Tribune

Yayinda yake kira ga kwantar da hankula da zaman lafiya a tsakanin mazauna Igangan da kewaye, Ministan ya ce dole ne a kama wadanda ke da hannu cikin 'yan bindigar tare da fuskantar fushin doka.

KU KARANTA: Tuna baya: Hotunan marigayi TB Joshua na aikin alheri sun bar mutane cikin jimami

A wani labarin, Kungiyar manoma Albasa da kasuwancinta a Najeriya (OPMAN) ta ce za ta katse samar da kayayyaki ga dukkan yankunan kudancin Najeriya daga ranar Litinin matukar gwamnatoci ba su amsa bukatun kungiyar ba.

Daily Trust ta tattaro cewa daya daga cikin bukatun OPMAN shi ne cewa membobin kungiyar da suka yi asara sakamakon rikicin kabilanci da addini a Kudancin dole ne a biya su yadda ya kamata.

Sauran sun hada da maido da doka da oda a wadannan yankuna tare da yin cikakken bincike don gano musabbabin wadannan hare-hare kan mambobinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.