Bayan korar dukkan kwamishinoninsa, gwamna Matawalle ya dawo da 3 daga cikinsu

Bayan korar dukkan kwamishinoninsa, gwamna Matawalle ya dawo da 3 daga cikinsu

- Rahoto ya bayyana cewa, gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya dawo da wasu kwamishinoninsa

- Hakazalika ya dawo da wasu shugabannin hukumomi na jihar bayan dakatar dasu a farkon watan Yuni

- Gwamnan ya bayyana wadanda aka dawo dasu cikin wata sanarwa da ya fitar a Gusau babban birnin jihar

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya amince da dawo da kwamishinoni uku da shugabannin hukuma uku na hukumomin jihar.

The Guardian ta ruwaito cewa a ranar 1 ga Yuni, Matawalle ya kori Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG) Alhaji Bala Bello da dukkan kwamishinoninsa 23 nan take.

Dawo dasu aikin na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Alhaji Kabiru Balarabe, shugaban ma’aikatan jihar kuma mukaddashin sakataren gwamnatin jihar a Gusau ranar Talata, The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: An yi kaca-kaca da kasuwar Abia, 'yan banga sun karbe dan kasuwa

Bayan fatattakar dukkan kwamishinoninsa, gwamna Matawalle ya dawo da wasu 3
Bayan fatattakar dukkan kwamishinoninsa, gwamna Matawalle ya dawo da wasu 3 Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Wadanda aka dawo da su din su ne Alhaji Ibrahim Dosara, Kwamishinan yada labarai, Alhaji Sufyanu Yuguda, Kwamishinan Kudi da Hajiya Fa’ika Ahmad, Kwamishiniyar Harkokin Jin Kai.

Matawalle ya ce an sake tura Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai na jihar, Alhaji Alhaji Abubakar S / Pawa.

Sauran sun hada da Abubakar Sodangi, shugaban gudanarwa na hukumar zakka da bada tallafi da kuma Alhaji Ali Muhammad-Dama, shugaban gudanarwa na hukumar tara kudaden shiga.

KU KARANTA: Zan karfafa muku cin naman Alade a madadin na Shanu, Akeredolu ga 'yan jiharsa

A wani labarin, Gwamnan jihar Zamfara, Bello Mohammed a ranar Talata ya ziyarci hedkwatar rundunar ‘yan sanda ta jiharsa, inda ya roki jami’an da su aiwatar da umarnin gani-a-harbe da Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar don magance matsalar rashin tsaro a kasar.

A watan Maris, Shugaba Buhari ya umarci hukumomin tsaro su harbe duk wanda aka gani da bindiga AK-47 yayin da ya ba da umarnin murkushe ‘yan bindiga, lamarin da ya jawo cece-kuce, in ji Premium Times.

Ya kuma jaddada a ranar 11 ga Maris cewa shugabannin tsaro sun karbi umarnin yin fata-fata da masu aikata laifuka, gami da harbin duk wanda aka samu da mallakar bindiga ba bisa doka ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.