Da duminsa: Majalisa za ta bincika dalilin hana Twitter, ta gayyaci Lai Mohammed

Da duminsa: Majalisa za ta bincika dalilin hana Twitter, ta gayyaci Lai Mohammed

Majalisar Wakilai ta zartar da bincike kan shawarar da Gwamnatin Tarayya ta yi na hana ayyukan Twitter a Najeriya.

Ta ce za ta kuma yi la’akari da tsarin shari’ar da Gwamnatin Tarayya ta bi wajen yanke hukunci a kai, The Nation ta ruwaito.

Najeriya a ranar Juma’a ta dakatar da ayyukan Twitter, kwanaki biyu bayan da kamfanin na sada zumunta ya cire wani rubutu na Shugaba Muhammadu Buhari wanda ya yi barazanar hukunta masu rigimar ballewa daga Najeriya, Reuters ta ruwaito.

Kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da abokan aikinsa kan ci gaba da zaman majalisar bayan hutun makonni biyu.

Da duminsa: Majalisa za ta bincika dalilin hana Twitter, ta gayyaci Lai Mohammed
Da duminsa: Majalisa za ta bincika dalilin hana Twitter, ta gayyaci Lai Mohammed Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Shugaban majalisar ya ce kwamitocin majalisar da abin ya shafa na sadarwa, shari’a da doka da kuma bayani, za su gabatar da rahoto a cikin kwanaki 10 don ba majalisar damar yanke hukunci kan haramcin.

Gbajabiamila ya ce yayin da shafin twitter ya kasance muhimmiyar hanyar sadarwa da kasuwanci ga matasa masu tasowa na Najeriya, gwamnati na da alhakin tabbatar da cewa ba ayi amfani da shi wajen lalata tsaron kasa ba.

Binciken shine a gano ko an bi ka'idoji wajen yanke shawara.

Shi ma Ministan Watsa Labarai da Al'adu, Lai Mohammed, za a gayyace shi don yi wa Majalisar bayani kan shawarar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel