Da dumi-dumi: Jami'ar Kaduna ta KASU ta dakatar da karatun digiri na farko

Da dumi-dumi: Jami'ar Kaduna ta KASU ta dakatar da karatun digiri na farko

- Jami'ar Jihar Kaduna ta bayyana dakatar da shirye-shiryen karatun digiri na farko a jami'ar

- Hakazalika ta bayyana wasu shirye-shirye da ta amince a ci gaba da yinsu a makarantar

- Sanarwar na zuwa ne bayan rikicin da ya barke tsakanin iyayen dalibai da gwamnatin jihar

Hukumar gudanarwar Jami'ar Jihar Kaduna (KASU) ta bayyana cewa, ta dakatar da ayyukan karatu na daliban digiri na farko a makarantar zuwa wani lokacin da ba ta ayyana ba.

Sai dai, hukumar gudanarwar ta bayyana wasu fannonin karatun da ba ta dakatar dasu ba, kamar yadda yazo a sanarwar da ta fitar a yau Talata 8 ga watan Yunin 2021.

Cikin wata sanarwa da Legit.ng Hausa ta samu, hukumar gudanarwar ta KASU ta fidda sanarwar mai nuni da dakatar da ayyukan karatu, amma ta umarci ma'aikatan makarantar da su ci gaba da zuwa aiki kamar yadda suka saba.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: An yi kaca-kaca da kasuwar Abia, 'yan banga sun karbe dan kasuwa

Da dumi-dumi: Jami'ar Kaduna ta KASU ta dakatar da karatu sai baba ya gani
Da dumi-dumi: Jami'ar Kaduna ta KASU ta dakatar da karatu sai baba ya gani Hoto: Kaduna State University, KASU Kaduna
Asali: Facebook

Sanarwar ta karanta:

"Hukumar gudanarwar jami'ar jihar Kaduna tana sanar da ma'aikata, dalibai da sauran jama'a cewa an dakatar da ayyukan karatun daliban digiri na farko har sai an gani.
"Shirye-shiryen karatun gaba da da digiri na farko, kwalejin likitanci, ilimin kimiyyar magunguna da karatun lokac-lokaci za su ci gaba da ayyukansu.
"Hakanan ana sa ran ma’aikata za su zo aiki kamar yadda suka saba.
"Gudanarwa zai magantu kan duk wani ci gaba da aka samu."

A baya an samu dambarwar da ta barke tsakanin iyayen dalibai a jihar Kaduna da kuma gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Nasir El-rufa'i, dangane da karin kudin makaranta da a cewarsu ya wuce hankali, BBC ta rahoto.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun gaji, Sheikh Gumi ya bayyana yanayin da 'yan bindiga ke ciki

A wani labarin, Daliban Jami'ar Jihar Kaduna, KASU, a ranar Talata sun tare babban titin zuwa gidan gwamnati a Kaduna, babban birnin jihar don yin zanga-zanga kan karin kudin makaranta da gwamnatin jihar ta yi, Channels Television ta ruwaito.

Jami'ar mallakar gwamnatin jihar ta sanar da karin kudin makaranta da kimanin 600% daga N26,000 da aka saba biya a baya.

A cewar sabon tsarin kudin makarantar da aka gabatar, yan jihar za su rika biyan N150,000 yayin da abokan karatunsu a bangaren likitanci da kimiyya za su rika biyan N170,000 zuwa sama duk shekara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel