'Yan bindiga sun gaji, Sheikh Gumi ya bayyana yanayin da 'yan bindiga ke ciki

'Yan bindiga sun gaji, Sheikh Gumi ya bayyana yanayin da 'yan bindiga ke ciki

- Fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Gumi ya bayyana yanayin da 'yan bindiga ke ciki

- A cewarsa, tuni 'yan bindigan sun gaji kuma suna son zaman tattaunawa domin su mika wuya

- Hakazalika ya bayyana cewa, dukkansu a shirye suke domin su aje makami idan sun samu yadda suke so

Sheikh Ahmad Gumi, wani malamin addinin Islama, kuma tsohon hafsan soji, a ranar Talata, ya bayyana cewa 'yan bindiga sun gaji kuma suna son a wanzar da zaman lafiya, PM News ta ruwaito.

Shehun malamin addinin musuluncin wanda ke zaune a Kaduna yayin tattaunawa da manema labarai ya ce 'yan bindigar a shirye suke su ajiye makamansu idan suka samu hadin kai na gaske daga gwamnati.

A cikin kalaman nasa: “Eh, gaskiya ne sosai saboda 'yan bindiga suna cewa yanayi ne ya ingiza su zuwa zama 'yan bindiga.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: An yi kaca-kaca da kasuwar Abia, 'yan banga sun karbe dan kasuwa

'Yan bindiga sun gaji, Sheikh Gumi ya bayyana yanayin da 'yan bindiga ke ciki
'Yan bindiga sun gaji, Sheikh Gumi ya bayyana yanayin da 'yan bindiga ke ciki Hoto: dailytrust.com
Asali: Facebook

“Idan suna da aboki na kwarai, a shirye suke su aje makamansu; sun gaji kuma suna son zaman lafiya.

“Dangane da ayyukansu, za ku fahimci cewa ko da sojoji suna fada kuma an ayyana tsagaita wuta, yakan dauki lokaci mai tsawo kafin su daina yakin.

“Muna iya ganin kusan 80% cikin 100% na manyansu sannan da wasu kananan kungiyoyi wadanda suka balle wadanda ba za mu iya haduwa da su ba saboda yanayi domin ba za mu iya sake shiga daji ba.

“Amma gaba daya, a shirye suke don zaman lafiya, a zahiri, mun tattara wakilansu, mun tattauna da su, kuma sun ce a shirye suke amma suna bukatar kawancen gaske. Siyasa ce musabbabin wannan lamarin.”

'Yan bindiga na ci gaba da barna a Najeriya, musamman yankin Arewa Maso Yammacin kasar, lamarin da ya kai ga sace-sacen dalibai da hallaka mutane da dama.

Sheikh Gumi, shine malamin da ya shahara wajen tattauna da 'yan bindigan, in da yake shiga daji don zaman tattaunawa tare da su.

A watan Fabrairu, Gumi ya gana da 'yan bindigan da suka sace daliban Kagara, in da ya tattauna dasu don jin matsalolinsu, The Guardian ta ruwaito.

KU KARANTA: Majalisa: Gwamnan CBN, IGP, NSA sun raina mu, shi yasa suka ki amsa gayyatarmu

A wani labarin, Gwamnan jihar Zamfara, Bello Mohammed a ranar Talata ya ziyarci hedkwatar rundunar ‘yan sanda ta jiharsa, inda ya roki jami’an da su aiwatar da umarnin gani-a-harbe da Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar don magance matsalar rashin tsaro a kasar.

A watan Maris, Shugaba Buhari ya umarci hukumomin tsaro su harbe duk wanda aka gani da bindiga AK-47 yayin da ya ba da umarnin murkushe ‘yan bindiga, lamarin da ya jawo cece-kuce, in ji Premium Times.

Ya kuma jaddada a ranar 11 ga Maris cewa shugabannin tsaro sun karbi umarnin yin fata-fata da masu aikata laifuka, gami da harbin duk wanda aka samu da mallakar bindiga ba bisa doka ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel