Gwamnan Zamfara Ya Tunkari Hedkwatar 'Yan Sanda Kan Dokar Harbe Masu Rike AK-47

Gwamnan Zamfara Ya Tunkari Hedkwatar 'Yan Sanda Kan Dokar Harbe Masu Rike AK-47

- Gwamnan jihar Zamfara ya ziyarci hedkwatar 'yan sanda a jihar don jaddada bukatar shugaba Buhari na harbe masu AK-47

- Ya bayyana bukatar aiwatar da bukatar shugaba Buhari na a harbe duk wanda aka gani da bindiga AK-47 ko makami

- Ya ce yana goyon bayan kudurin gwamnatin Buhari na kokarin wanzar da zaman lafiya da kare dukiyoyin 'yan kasa

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Mohammed a ranar Talata ya ziyarci hedkwatar rundunar ‘yan sanda ta jiharsa, inda ya roki jami’an da su aiwatar da umarnin gani-a-harbe da Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar don magance matsalar rashin tsaro a kasar.

A watan Maris, Shugaba Buhari ya umarci hukumomin tsaro su harbe duk wanda aka gani da bindiga AK-47 yayin da ya ba da umarnin murkushe ‘yan bindiga, lamarin da ya jawo cece-kuce, in ji Premium Times.

Ya kuma jaddada a ranar 11 ga Maris cewa shugabannin tsaro sun karbi umarnin yin fata-fata da masu aikata laifuka, gami da harbin duk wanda aka samu da mallakar bindiga ba bisa doka ba.

KU KARANTA: Tsageru Sun Kashe Shugaban Matasan PDP a Imo, Sun Kona Gidansa Da Motoci

Wata sanarwa wanda kakakin gwamnan, Jamilu Magaji ya fitar ta ce:

"A lokacin ziyarar, gwamnan ya sake jaddada umarnin cewa 'yan sanda da sauran jami'an tsaro na gwamnati su aiwatar da umarnin shugaban kasa yadda ya kamata na harbin duk wani dan bindiga, tilo ko gungun mutane da aka gani da AK-47 ko wani makami."

A cewar gwamnan, wadanda doka ta amince da su ko kuma hukumomin tsaro ne kadai ke da hakkin rike bindigogi da sauran manyan makamai inda ya ce wadanda aka samu da mallakar bindiga ba bisa ka'ida ba ya kamata a harbe su nan take, Channels Tv ta ruwaito.

Matawalle ya ce gwamnatinsa tana matukar goyon baya ga manufofi da shirye-shiryen Shugaba Buhari, musamman a kokarinsa na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.

KU KARANTA: Za Ku Shiga Firgici: Shugaba Buhari Ya Kalubalanci Masu Kitsa Kifar Da Gwamnatinsa

Gwamnan Zamfara Ya Tunkari Hedkwatar 'Yan Sanda Kan Wata Doka
Gwamnan Zamfara Ya Tunkari Hedkwatar 'Yan Sanda Kan Wata Doka Hoto: theshieldg.com
Asali: UGC

A wani labarin, 'Yan bindiga da suka sace daliban makarantar Salihu Tanko Islamiyya da ke garin Tegina a karamar hukumar Rafi ta jihar Neja sun tuntubi shugabannin makarantar.

'Yan bindigan sun tuntubi shugaban makarantar, Alhaji Abubakar Alhassan, da misalin karfe 4 na yamma a ranar Litinin, inda suka nemi ya biya N110m a matsayin kudin fansa don sakin daliban.

Da yake magana da manema labarai ta wayar tarho a ranar Talata, Alhassan ya ce 'yan bindigan sun yi ikirarin suna da yara 156 a hannunsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel