Da dumi-dumi: An yi kaca-kaca da kasuwar Abia, 'yan banga sun karbe dan kasuwa

Da dumi-dumi: An yi kaca-kaca da kasuwar Abia, 'yan banga sun karbe dan kasuwa

- Rahotanni daga jihar Abia na bayyana cewa, rikici y barke tsakanin 'yan kasuwa da 'yan banga

- An hallaka wani dan kasuwa har lahira, yayin da aka yi kaca-kaca da kasuwar a jihar ta Abia

- Gwamnayin jihar ta yi Allah wadai da wannan rikici, ta kuma bayyana cewa za ta yi bincike

Yanzu haka ana hargitsi a kasuwar katako ta Umuahia da ke kan titin Ahiaeke a jihar Abia.

Daily Trust ta gano cewa rikicin ya barke ne bayan ’yan kasuwa sun ki biyan harajin N18,000 da Hukumar Haraji ta Jihar Abia ta sanya.

Wani mazaunin ya ce hukumar tara kudaden shiga ta jihar ta umarci ‘yan kasuwar da suka ki biyan harajin da su rufe shagunansu.

Sai dai, 'yan kasuwar sun mai da martani yayin da 'yan banga suka zo kasuwar don aiwatar da umarnin.

KU KARANTA: Majalisa: Gwamnan CBN, IGP, NSA sun raina mu, shi yasa suka ki amsa gayyatarmu

Da dumi-dumi: An yi kaca-kaca da kasuwar Abia, 'yan banga sun karbe dan kasuwa
Da dumi-dumi: An yi kaca-kaca da kasuwar Abia, 'yan banga sun karbe dan kasuwa Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Mazaunin ya ce yayin artabun, ‘yan banga sun harbe daya daga cikin 'yan kasuwan da aka bayyana da suna ‘Indomie’, wanda daga baya ya mutu yayin da wasu 5 suka samu raunuka.

Matakin da dan bangan ya dauka ya harzuka 'yan kasuwan wadanda suka rama ta hanyar kona ofishi da motocin 'yan bangan.

Gwamnatin Jihar Abia ta mayar da martani game da rikicin, inda ta yi Allah wadai da barnata Ofishin ‘Yan bangan da Kasuwar Katakon.

A cikin wata sanarwa, Sakataren Gwamnatin Jihar, Chris Ezem, ya nemi ’yan sanda su fara bincike kan lamarin.

Gwamnati ta umarci jami'an 'yan banga na Abia su fice daga kasuwar, yayin da aka umarci shugabannin kasuwar da su taimaka wa 'yan sanda su gano masu kone-konen.

KU KARANTA: Badakalar Abacha: Makudan kudaden da Najeriya ta kwato cikin shekaru 23

A wani labarin, Gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, ya ce gwamnatinsa za ta karfafa cin naman alade a madadin naman shanu don tattala miliyoyin nairorin da jihar ke asara ga sauran jihohin da ke samar da naman shanu da sauran nau'ikan nama, Daily Trust ta ruwaito.

Akeredolu ya fadi haka ne a ranar Litinin yayin kaddamar da wani babban mayankar alade ta Dutchman Piggery da kayan tallafi a Ilutoro da ke karamar hukumar Akure ta Arewa a jihar a matsayin wani bangare na ayyukan cikarsa kwanaki 100 a ofis.

A cewar gwamnan, kudin da ake kashewa ga wasu jihohin da ke samar da shanu da sauran nau'ikan nama zasu kasance a jihar don kara tattalin arzikin jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel