Majalisa: Gwamnan CBN, IGP, NSA sun raina mu, shi yasa suka ki amsa gayyatarmu

Majalisa: Gwamnan CBN, IGP, NSA sun raina mu, shi yasa suka ki amsa gayyatarmu

- Kwamitin dake bincike kan kudaden da aka kwato ya fusata da wasu jami'an gwamnati

- Kwatin ya ce lallai akwai raini cikin lamarin, don haka ya ba da wa'adin awanni 72 su hallara a gabansa

- Ya kuma ce idan har ba za a mutunta kiran majalisa ba, to babu amfanin majalisar kwata-kwata

Wani dan majalisar wakilai, Isiaka Ibrahim, a ranar Litinin ya koka kan yadda Shugabannin gwamnati suka ki bayyana yayin binciken kudaden da aka kwato, Channels Tv ya ruwaito.

Kwamitin wucin gadi na majalisar yana bincikar yadda hukumomin gwamnati suka sarrafa badakalar da aka kwato.

Ibrahim wanda mamba ne a Kwamitin wucin gadi akan kudaden da aka kwato ya koka kan rashin halartar Shugaban Gwamnatoci rashin girmamawa ne ga Majalisar Kasar.

KU KARANTA: Badakalar Abacha: Makudan kudaden da Najeriya ta kwato cikin shekaru 23

Majalisa: Gwamnan CBN, IGP, NSA sun raina mu, shi yasa suka ki amsa gayyatarmu
Majalisa: Gwamnan CBN, IGP, NSA sun raina mu, shi yasa suka ki amsa gayyatarmu Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Kwamitin wucin gadi ya baiwa Gwamnan Babban Bankin, Godwin Emefiele, da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno, awanni 72 su bayyana a gaban sa.

Kwamitin ya kuma bayar da irin wannan wa'adin ga Sufeto Janar na 'yan sanda, Usman Alkali, da Darakta-Janar na Hukumar Kula da Tattalin Arziki ta Najeriya, NIMASA, Bashir Jamoh, Premium Times ta ruwaito.

An gabatar da sammacin ne a ranar Litinin, bayan Mista Emefiele da sauran sun kasa bayyana a gaban kwamitin.

Jami'an na gwamnati sun tura wakilai, amma shugaban kwamitin, Adejoro Adeogun (APC, Ondo), ya ce sun kasa tura wasiku don sanar da hakan.

Ibrahim ya kara da cewa 'yan majalisar babu amfanin kasancewarsu a cikin majalisar idan hukumomin gwamnati suka ki mutunta cibiyar da ta samar da su.

KU KARANTA: Lai Mohammed ya caccaki masu lalata kadarorin gwamnati, ya ce 'yan ta'adda ne

A wani labarin, Lai Mohammed, Ministan yada labarai na Najeriya, ya bayyana karara cewa ‘yan Najeriya da suka shiga shafin Twitter, ciki har da Fasto Enoch Adeboye, ya kamata su jira gurfanarwa.

Lai Mohammed ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Africa Focus a ranar Litinin lokacin da aka tambaye shi ko za a gurfanar da Mista Adeboye saboda amfani da Twitter.

Lai Mohammed ya ce: "To Babban Lauya ya bayyana a fili cewa idan wani ya karya doka, za a hukunta wannan mutumin."

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.