Sarkin Musulmi: Wasu Tsirarun 'Sheɗanun' Manyan Mutane Na Ƙoƙarin Tarwatsa Nigeria

Sarkin Musulmi: Wasu Tsirarun 'Sheɗanun' Manyan Mutane Na Ƙoƙarin Tarwatsa Nigeria

- Sarkin Musulmi, mai alfarma Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya ce wasu manyan mutane na shirin tarwatsa Nigeria don cimma wata manufa ta su

- Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne a jawabin da ya yi wurin kaddamar da sansanin maniyatta a jihar Bauchi

- Sultan din ya bukaci yan Nigeria su hada hannu wuri guda su yi rajista a zabe, su fita suyi zabe su kuma kare kuri'unsu don zaben shugabanni nagari

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar na III, ya ce wasu tsirarun manyan mutane a Nigeria da ke tunanin dole sune za su rika juya kasar suna kokarin tarwatsa kasar, Daily Trust ta ruwaito.

The Nation ta ruwaito cewa Sultan din wanda ya yi wannan furucin a ranar Litinin a Bauchi yayin kaddamar da sansanin maniyatta aikin hajji ya ce akwai bukatar daukan matakin gaggawa domin karfafa gwiwar yan Nigeria domin akwai 'shedanu' da yawa a kasar.

Sarkin Musulmi: Wasu Manyan Mutane Suna Shirin Tarwatsa Nigeria
Sarkin Musulmi: Wasu Manyan Mutane Suna Shirin Tarwatsa Nigeria. Hoto: @daily_trust
Asali: UGC

DUBA WANNAN: El-Rufai Ya Ɗauki Sabbin Ma'aikata '10,000' a Yayin Da Jihar Ke Rage Ma'aikata

Ya ce, "Wasu mutane suna nan sun dage sai sun tarwatsa kasar kuma na yi imanin ya kamata mu mike tsaye mu kallubalanci wannan tsirarun manyan mutanen da ke tunanin dole sune za su rika juya kasar.

"Ya kamata mutanen kasar su sani cewa akwai rawar da za mu iya takawa, muma masu ruwa da tsaki ne kuma babu wanda zai iya tilasta mu yin abin da suke so ba tare da goyon bayan mu ba.

"Shi yasa a lokacin da dan uwana Sheikh Yahaya Sani Jingir ya ce kuri'arka ne yancin ka kuma za ku iya canja kowane gwamnati, abin da ya rage kawai shine ku yi rajista, ku yi zabe a ranar zabe kuma kada ku bari kowa ya sace muku kuri'un ku.

"Lokaci ya yi da za ku sake dabara da tsari domin samun ingantancen shugabanci a kasar nan."

Sultan din ya yi bayanin cewa Allah ne ke bada shugabancin, yana mai kara cewa "Yana tsammanin mu yi adalci ga kowa.

"Mu sani cewa wata rana zamu amsa tambayoyi kan yadda muka gudanar da shugabancin mu a gobe kiyama.

"Yana da kyau mu sauke nauyin da aka dora mana iya gwargwadon ikonmu mu barwa Allah sauran."

A wani labarin daban, daliban makarantun sakandare a jihar Kano sun yi kira ga gwamnatin jihar ta samarwa dalibai mata audugan mata kamar yadda ta ke samar da littafan karatu kyauta, Vanguard ta ruwaito.

Daliban sun koka da cewa yan mata da yawa ba su da kudin siyan audugan matan, don haka suke rokon gwamnatin ta taimaka musu domin su samu su rika tsaftace kansu.

Sun yi wannan rokon ne yayin wani taron wayar da kai na kwana daya da aka yi kan tsaftar mata da jiki da Kungiyar Yan Jarida Masu Rahoto Kan Bangaren Lafiyar Mata reshen jihar Kano suka shirya don bikin ranar Al'adar Mata Ta Duniya na 2021'

Asali: Legit.ng

Online view pixel