2023: Babu sunan Tinubu yayinda kungiyar arewa tace tana duba yiwuwar marawa Amaechi, Umahi da sauransu baya

2023: Babu sunan Tinubu yayinda kungiyar arewa tace tana duba yiwuwar marawa Amaechi, Umahi da sauransu baya

- Kungiyar nan ta Arewa Mandate Initiative (AMI) ta nuna goyon bayanta ga kiraye-kirayen da ake yi na mulkin karba-karba a Najeriya

- AMI ta bayyana matsayinta a ranar Alhamis, 3 ga watan Yuni, a Abuja, bayan tattaunawa da wasu shugabannin arewa

- A cewar kungiyar, zai zama adalci idan arewa ta kyale kudu ta samar da wanda zai gaji Shugaba Muhammadu Buhari a 2023

Kungiyar hadin kan kungiyoyin arewa, Arewa Mandate Initiative (AMI), ta bayyana cewa a halin yanzu arewa na la’akari da wasu ‘yan siyasan kudu da zasu samu goyon bayan su a babban zaben na 2023.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa gamayyar kungiyar ta ce akasarin ‘yan arewa sun himmatu ga tunanin mulkin karba-karba tsakanin arewa da kudu.

KU KARANTA KUMA: Yan bindigar da suka sace 'yan makarantar Neja sun kara kudin fansa daga N110m zuwa N200m

2023: Babu sunan Tinubu yayinda kungiyar arewa tace tana duba yiwuwar marawa Amaechi, Umahi da sauransu baya
2023: Babu sunan Tinubu yayinda kungiyar arewa tace tana duba yiwuwar marawa Amaechi, Umahi da sauransu baya Hoto: @ChibuikeAmaechi, @realRochas
Asali: Twitter

Legit.ng ta tattaro cewa kungiyar ta bayyana hakan ne a garin Abuja a ranar Alhamis, 3 ga watan Yuni, a cikin wata sanarwa da jagoranta, Muhammed Mubarak, da sakataren, Aminu Muhammed suka fitar a Abuja.

KU KARANTA KUMA: Gumi ga FG: Ku sasanta da yan bindigar da suka tuba, ku yi amfani da su wajen yakar wadanda suka ki saduda

Kudu ne ya kamata ya samar da shugaban Najeriya na gaba

AMI ta kuma lura da cewa tattaunawa tsakanin kungiyoyin siyasa da yawa, musamman a kan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a arewa a cikin watanni ukun da suka gabata sun nuna shaidar jajircewa wajen tabbatar da cewa shugaban Najeriya na gaba ya fito daga yankin kudancin kasar. .

A cewar sanarwar, Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi; da ministan man fetur, Timipre Sylvia; suna daga cikin fitattun ‘yan takara daga kudu maso kudu da za su iya maye gurbin Shugaba Muhammadu Buhari a 2023.

Hakanan ya kara da cewa tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha da gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi suna daga cikin ‘yan takarar shugaban kasa daga yankin kudu maso gabas.

Magajin Buhari na iya fitowa daga kudu maso kudu ko kudu maso gabas

Jerin sunayen yan takarar daga kudu maso kudu da kuma kudu maso gabas a cewar kungiyar sune:

1. Ministan Sufuri - Rotimi Amaechi

2. Ministan kasa, man fetur - Cif Timipre Sylvia

3. Tsohon shugaban majalisar dattawa - Victor Ndoma Egba

4. Tsohon gwamnan jihar Imo - Rochas Okorocha

5. Ministan kimiyya da fasaha - Ogbomnaya Onu

6. Gwamnan jihar Ebonyi - David Umahi

A wani labarin, Samuel Ortom, gwamnan jihar Benuwe, ya yi ikirarin cewa wasu gwamnoni da wasu mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ne saboda suna tsoron kada EFCC ta gurfanar da su.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa gwamnan ya yi wannan zargin ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Filin jirgin saman Makurdi yayin da yake dawowa daga tafiya zuwa jihar Oyo inda ya ziyarci Gwamna Seyi Makinde don kaddamar da ayyukansa.

Ya nuna kwarin gwiwar cewa sauya shekar ba zai haifar da wani mummunan tasiri ba a kan jam'iyyar adawa, kamar yadda jaridar New Telegraph ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng