Yan bindigar da suka sace 'yan makarantar Neja sun kara kudin fansa daga N110m zuwa N200m

Yan bindigar da suka sace 'yan makarantar Neja sun kara kudin fansa daga N110m zuwa N200m

- Maharan da suka yi garkuwa da daliban makarantar Neja sun kara yawan kudin fansar da suke so a biya

- A yanzu suna neman a biya naira miliyan 200 maimakon miliyan 110 da aka tsayar a baya

- Abubakar Alhassan, babban malamin makarantar kuma mahaifi ga yara biyu daga cikin yaran da aka sace, ya bayyana hakan

'Yan bindiga sun nemi a biya su Naira miliyan 200 kudin fansa kafin su sako daliban Islamiyya 156 da aka sace a jihar Neja.

A ranar 27 ga watan Mayu, 'yan bindiga sun kai hari makarantar Salihu Tanko Islamiyya da ke garin Tegina, karamar hukumar Rafi, suka yi awon gaba da wasu 'yan makaranta.

KU KARANTA KUMA: Dukanmu muna da laifi, in ji Obasanjo kan halin da Najeriya ke ciki

Yan bindigar da suka sace 'yan makarantar Neja sun kara kudin fansa daga N110m zuwa N200m
Yan bindigar da suka sace 'yan makarantar Neja sun kara kudin fansa daga N110m zuwa N200m Hoto: @channelstv
Asali: UGC

Da farko 'yan fashin sun nemi kudin fansa na naira miliyan 110 kan daliban da aka sace.

Sai dai kuma, lamarin ya dauki sabon salo domin 'yan fashin sun daukaka bukatar su zuwa Naira miliyan 200, jaridar The Cable ta ruwaito.

Abubakar Alhassan, babban malamin makarantar kuma mahaifi ga yara biyu daga cikin yaran da aka sace, ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da Arise TV ranar Juma’a.

"Sun ce kada ma na sake magana game da Naira miliyan 110 sai na miliyan 200," in ji shi.
“Ina rokon su amma ba su saurara ba. Sun yanke wayar kuma ban ji daga garesu ba.”

A nata bangaren, Hadiya Hashim, wata uwa da ke da yara uku da aka sace, ta koka game da mummunan halin da daliban ke ciki.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An tabbatar da Alkali Baba a matsayin sufeto janar na ‘yan sanda

Ta ce yaran sun kwana uku suna fama da yunwa kuma an hana su ruwa.

“Yanayin da yaran nan suke ciki, ba za ku iya tunaninsu ba. Ka san ba su da gidaje a daji. Da farko, karamin rahoton da muka samu, a ranar Litinin, ya ce sun ajiye yaran a karkashin wata babbar bishiya kuma sun kwana uku ba tare da ba su ruwa ba, ” inji ta.

A baya mun ji cewaal’umman garin Tegina, inda aka sace yara masu yawa sun fara tattara kudi domin ceto daliban Islamiyya da aka sace.

Shugaban makarantar Islamiyya, Salihu Tanko Abubakar Alhassan, ya ce wadanda suka sace yaran sun fara dukan yaran da ke hannunsu harma wasu basa iya tafiya.

Shugaban makarantar Islamiyyar, ya bayyana a cikin wata hira da aka yi da shi a gidan talbijin na Arise TV wanda jaridar The Nation ta bibiya cewa an sace uku daga cikin malamansa da suka hada da mata biyu da kuma namiji daya tare da yaran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng