Gwamnan PDP ya bayyana dalilin da yasa takwarorinsa ke komawa APC
- Gwamna Ortom ya yi ikirarin cewa wasu gwamnonin PDP da suka sauya sheka zuwa APC sun yi hakan ne don gudun kada EFCC ta gurfanar da su
- Gwamnan na Benuwai ya bugi kirjin cewa ficewar ba zai kawo cikas ga damar da PDP ke da shi na karbar mulki a 2023 ba
- A cewar Ortom, gazawar APC za su ba PDP damar fitar da jam’iyya mai mulki a zabubbuka masu zuwa
Samuel Ortom, gwamnan jihar Benuwe, ya yi ikirarin cewa wasu gwamnoni da wasu mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ne saboda suna tsoron kada EFCC ta gurfanar da su.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa gwamnan ya yi wannan zargin ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Filin jirgin saman Makurdi yayin da yake dawowa daga tafiya zuwa jihar Oyo inda ya ziyarci Gwamna Seyi Makinde don kaddamar da ayyukansa.
KU KARANTA KUMA: Dukanmu muna da laifi, in ji Obasanjo kan halin da Najeriya ke ciki
Ya nuna kwarin gwiwar cewa sauya shekar ba zai haifar da wani mummunan tasiri ba a kan jam'iyyar adawa, kamar yadda jaridar New Telegraph ta ruwaito.
Gwamna Ortom ya ce a yanzu da ‘yan Najeriya suka gwada PDP da APC, ba sa bukatar wani annabi daga sama ya fada musu jam’iyyar da za su zaba a 2023.
Gwamnan na jihar Benuwai wanda ya taba zama dan jam'iyyar APC ya yi ikirarin cewa jam'iyya mai mulki ba ta yi rawar gani ba.
KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya jagoranci taron majalisar ‘yan sanda
Kalamansa:
“Na kasance cikin Siyasa tun daga 1982, kuma babu abin da ban sani ba a cikin wannan wasan, don haka mafi yawan mutanen da suka sauya sheka a yanzu suna tsoron EFCC ne, kamar yadda kuka sani, tsohon shugaban APC, Adams Oshiomole ya taba sanarwa a bayyane cewa duk wanda ya sauya sheka zuwa APC an gafarta masa zunubinsa, amma a wurina ba na neman gafarar kowa, shi ya sa nake shawartar mutanena da su yi abin da ya dace."
Gwamna Ortom ya ce a karshe, babu wanda zai hana EFCC gurfanar da duk wanda ya aikata zamba.
Ya lura cewa gara masa ya koma kauyensa a matsayinsa na manomi da ya shiga cikin duk wani abu da zai jefa shi cikin matsala.
Gwamnonin PDP biyu da suka koma APC kwanan nan sune Dave Umahi na jihar Ebonyi da Ben Ayade na jihar Cross River.
A wani labarin, Sanata mai wakiltar yankin Bauchi ta Arewa a majalisar dattawa, Adamu Mohammed Bulkachuwa, ya yi magana game da yadda 2023 zai kasance.
Adamu Mohammed Bulkachuwa ya nuna cewa sam ba ya goyon-bayan tsarin karba-karba, ta yadda za a rika zagayawa da mulki tsakanin Kudu da Arewa.
Da yake magana a ranar Talata, 2 ga watan Yuni, 2021, Sanata Adamu Mohammed Bulkachuwa ya ce duk ‘dan siyasar da yake ganin zai kai labari, ya fito takara.
Asali: Legit.ng