Gumi ga FG: Ku sasanta da yan bindigar da suka tuba, ku yi amfani da su wajen yakar wadanda suka ki saduda

Gumi ga FG: Ku sasanta da yan bindigar da suka tuba, ku yi amfani da su wajen yakar wadanda suka ki saduda

- An shawarci gwamnatin tarayya kan yadda zata shiga cikin yan fashi da makami tare da cin galaba a kansu cikin dabara

- Shahararren malamin addinin musuluncin nan da ke zaune a Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi ne ya ba gwamnati shawarar

- Gumi yana son hukumomi su shigo cikin 'yan fashin tare da sa wadanda suka yi nadama su yaki wadanda ba su tuba ba

Shahararren malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi, ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta tallafawa kungiyoyin da suka balle a tsakanin 'yan fashi a matsayin wata hanya ta kawo karshen yawan sace-sacen daliban makaranta.

Gumi, wanda ya yi magana da jaridar Punch ta wayar tarho a ranar Laraba kan sace ‘yan makarantar Islamiyya 200 da ke karamar hukumar Rafi ta jihar Neja, ya ce‘ yan fashi da yawa sun shirya domin tattaunawa, ya kara da cewa gwamnati za ta iya amfani da su don yakar munanan.

KU KARANTA KUMA: Kawai mu rufe majalisar dokokin tarayya idan har ba za mu iya ceto kasar ba – Sanata Smart Adeyemi

Gumi ga FG: Ku sasanta da yan bindigar da suka tuba, ku yi amfani da su wajen yakar wadanda suka ki saduda
Gumi ga FG: Ku sasanta da yan bindigar da suka tuba, ku yi amfani da su wajen yakar wadanda suka ki saduda Hoto: Kola Sulaimon/AFP
Asali: Getty Images

Ya ce:

“Kullum muna yin iya bakin kokarinmu, amma kun gani, kuna bukatar hannu biyu don musabaha. Kun san wadannan mutanen ('yan fashi) suna bukatar tattaunawa daga gwamnatin kanta. Idan kuka sasanta dasu ba tare da sa hannun gwamnati ba, matsala ce.
“Ya kamata gwamnati ta kasance mai aiki da su. Muna da dayawa daga cikinsu wadanda a shirye suke da su yaki gurbatattun. Ku yi amfani da mara kyau don yaƙar mummunan, sannan kuyi amfani da mai kyau don yaƙar marasa kyau idan kuka gama da mummunan. Duba Boko Haram, wa ya gama da Shekau? Shin ba kungiyar da ta balle bane? Don haka, yana da sauki.
“Duk wadannan fafutukar da kuke gani, idan gwamnati za ta iya yin wani bangare kuma kungiyar da ta balle ta samu tallafi, kowane mutum na son mulki da kudi, za su yi aikinku. Akwai da yawa da a shirye suke da su sallama kansu. Duk wadanda ka ga na hadu da su a daji, suna gaya mana, ‘mun shirya.’ ”

KU KARANTA KUMA: Rundunar sojin kasa kadai ba za ta iya magance matsalar tsaron Najeriya ba – Shugaban hafsan soji

A halin da ake ciki, mun ji cewa miyagun 'yan ta'adda da ake zargin 'yan bindiga ne sun kai farmaki jihar Kano kuma sun tasa keyar wani attajirin dan kasuwa dake karamar hukumar Dambatta a jihar.

'Yan bindigan sun kai farmakin garin Kore a tsakar daren Alhamis inda suka dinga ruwan wuta babu sassauci, Daily Trust ta ruwaito.

Wannan mummunan hari yana zuwa ne bayan kwana daya da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano yayi korafin cewa miyagu sun fara tattaruwa a dajin Falgore dake jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng